Ilimi Kogi ne: Ganduje Ya Gano Abubuwan da Ke Jawo Yawan Sauya Sheka a Najeriya

Ilimi Kogi ne: Ganduje Ya Gano Abubuwan da Ke Jawo Yawan Sauya Sheka a Najeriya

  • Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya yi magana mai kama hankali game da siyasa a Najeriya
  • Ganduje ya abubuwan da ke haddasa yawaitar sauya sheƙar ƴan siyasa a Najeriya wanda ke jawo matsala
  • Tsohon gwamnan ya bukaci a ƙarfafa dimokuraɗiyyar cikin gida da siyasar da ta ta'allaka kan manufofi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya ja hankalin yan siyasa game da dimukradiyya.

Ganduje ya ce yawaitar sauya sheƙar ƴan siyasa tsakanin jam'iyyu na faruwa ne saboda rashin ingantacciyar akidar siyasa.

Ganduje ya magantu kan inganta dimokuraɗiyya
Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Twitter

Ganduje ya bayyana hakan a Abuja yayin ƙaddamar da littafi kan dimokuraɗiyya wanda ɗan jarida Onyekachi Eze-Opezulu ya rubuta, cewar Tribune.

Ganduje ya shawarci jam'iyyun siyasa

Ya ce kamata ya yi jam'iyyun siyasa su kasance masu ingantattun falsafa, tsare-tsare da manufofi waɗanda za su bambanta su daga sauran jam'iyyu.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya gana da Sanata Hanga yayin da ake shirin raba shi da Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano ya ce rashin fayyace akidar jam'iyyu ya ƙarfafa sauya sheƙa saboda muradun kai, ba saboda bin ƙa'idoji ko manufofin siyasa ba.

A cewarsa, wannan yanayi ya kuma sa ya zama da wahala ga ƴan ƙasa su bambance manufofin jam'iyyu domin yin zaɓi cikin fahimta.

Ganduje ya bukaci a ƙarfafa dimokuraɗiyyar cikin gida a jam'iyyu tare da inganta siyasar da ta ta'allaka kan batutuwa da manufofi masu amfani.

Ya ce dimokuraɗiyya ba gudanar da zaɓe kaɗai ba ce, domin tana buƙatar bin doka, tsarin mulki, hukumomin zaɓe masu inganci da zaɓe sahihi.

Ya ƙara da cewa kare waɗannan ginshiƙai zai tabbatar da zaman lafiyar siyasa, haɗin kan ƙasa da ci gaba mai ɗorewa a Najeriya.

Ganduje ya gano matsalolin sauya sheka a Najeriya
Tsohon shugaban APC a Najeriya, Abdullahi Ganduje. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Facebook

Ganduje ya tuna jam'iyyarsa ta baya

Ganduje ya tunatar cewa ya kasance mamba a PDP daga shekarar 1998 kafin ya sauya sheƙa zuwa APC a ƙarshen shekarar 2013, cewar Punch.

Shi ma Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ce littafin ya zo a kan lokaci wajen bayyana sauyin Najeriya daga mulkin soja zuwa dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Shugaba Tinubu zai samu gagarumar nasara a zaben 2027'

Idris ya ce littafin zai zama kayan wayar da kan jama'a da kuma muhimmin abin nazari ga masu bincike da al'ummomi masu son fahimtar tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.

Tsohon gwamnan Nasarawa, Tanko Al-Makura, ya ce littafin ya haɗa tarihin gwagwarmayar dimokuraɗiyya da darussa masu amfani ga shugabanni da ƴan siyasa.

Ya tuna cewa ya taba zama sakataren tsohuwar jam'iyyar NRC a Jamhuriya ta Uku, yana mai jaddada muhimmancin sanin tarihin siyasar ƙasa.

Al-Makura ya kuma bukaci ƴan Najeriya su ci gaba da kare da ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya ba tare da la'akari da bambancin siyasa, ƙabila ko addini ba.

Ganduje ya fadi dalilin barin Gawuna APC

Kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana dalilin da ya sa aka gan shi da shugaban ƙasa a kwanakin baya.

Ganduje ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya kira shi domin tattauna rikicin siyasar Kano da ta dauki zafi.

Tsohon gwamnan ya kuma yi magana game da sauya shekar tsohon mataimakin, Nasiru Yusuf Gawuna da tasirin hakan a siyasar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.