ADC Ta Fadi Yadda za Ta Kawo Karshen Mulkin Tinubu a 2027

ADC Ta Fadi Yadda za Ta Kawo Karshen Mulkin Tinubu a 2027

  • Jam'iyyar ADC ta bayyana kwarin gwiwar cewa tikitin Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi zai kayar da Bola Tinubu da Kashim Shettima
  • Mai magana da yawun jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce wahalar rayuwa, yunwa da rashin tsaro za su sa 'yan Najeriya su nemi sauyi a 2027
  • ADC ta kuma yi zargin cewa APC na shirin yin magudin zaɓe, amma ta ce al'umma za su kasance cikin shiri domin hana duk wata murdiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa tana da cikakken yaƙinin cewa haɗa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi, a tikitin shugaban ƙasa zai kayar da Bola Ahmed Tinubu.

Mai magana da yawun jam'iyyar na ƙasa, Malam Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da ya yi.

Kara karanta wannan

An sako Tinubu a gaba ya yi murabus kafin zaben 2027 bayan rahoton Bankin Duniya

Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar
Bola Tinubu a hagu da Atiku Abubakar a dama. Hoto: Paul O. Ibe|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Yayin tattaunawa da Tribune, Bolaji Abdullahi ya ce ADC ce kaɗai ke wakiltar sahihin sauyi a halin yanzu, saboda haka ne jam'iyyar ke da kwarin gwiwar cewa tikitin Atiku da Amaechi zai samu nasara a babban zaɓen 2027.

ADC ta hango nasara a 2027

Bolaji Abdullahi ya ce 'yan Najeriya ne za su yanke hukuncin cire gwamnatin APC daga mulki saboda wahalhalun da suka fuskanta a cikin shekaru ukun gwamnatin Shugaba Tinubu.

Ya bayyana cewa matsalolin rashin tsaro, yunwa da talauci sun nuna gazawar gwamnatin APC wajen magance matsalolin ƙasar.

A cewarsa, wani rahoto ya nuna cewa kusan mutum miliyan 17 a Najeriya na cikin matsalar yunwa, yana mai cewa irin wannan matsala ba ta taɓa faruwa ba a tarihin ƙasar.

Zargin magudin zabe a 2027

Da aka tambaye shi abin da ya ba su kwarin gwiwar cewa tikitin Atiku da Amaechi zai kayar da Tinubu da Shettima, Bolaji Abdullahi ya ce al'ummar Najeriya ne za su cire shugaban daga mulki.

Kara karanta wannan

ADC: Abubakar Malami ya zabi abokin takarar gwamnan Kebbi a 2027

Ya ce yana da wuya 'yan Najeriya su sake zaɓar gwamnatin da, a cewarsa, ta jefa su cikin wahalhalu a tsawon shekaru uku da suka gabata.

Bolaji Abdullahi na ADC
Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi yana jawabi. Hoto: Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Har ila yau, ya yi zargin cewa APC na shirin yin magudin zaɓen 2027, amma ya ce 'yan Najeriya za su kasance cikin shiri domin kare ƙuri'unsu.

Bolaji Abdullahi ya kuma yaba da matakin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) na ƙara wa'adin sanya sunayen 'yan takara bayan roƙon da IPAC ta yi.

A ranar 16 ga Yulin 2026 ma dai Vanguard ta rahoto Bolaji Abdullahi na cewa ADC za ta fatattaki Bola Tinubu a zaben 2027.

Ana sa bayanan 'yan takara

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APC ta fara sanya sunayen 'yan takararta na gwamna da 'yan majalisar dokokin jihohi a shafin INEC domin shirye-shiryen zaɓen 2027.

Rahotanni sun nuna cewa jam'iyyar ta riga ta sanya sunayen gwamnoni 16 masu neman wa'adi na biyu, yayin da sashen fasahar sadarwa (ICT) na APC ke ci gaba da aiki.

A bisa jadawalin da hukumar INEC ta fitar, za a gudanar da zaɓen gwamnoni da 'yan majalisar dokokin jihohi a ranar 6 ga Fabrairun shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng