Ganduje Ya Fadi Abin da zai Hana Obi da Atiku Buge Tinubu a 2027
- Tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, yi wa 'yan takarar shugaban kasa, Peter Obi da Atiku Abubakar kaca-kaca
- Ya tunatar da su cewa Arewa na taka muhimmiyar rawa wajen tantance wanda zai zama shugaban kasa, kuma ba su da wannan karfin a shiyyar
- Ganduje, wanda tsohon gwamnan ne sau biyu a jihar Kano ya yi hasashen yadda babban zaben 2027 yayin da yan adawa ke kokarin kwace mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce 'yan takarar shugaban kasa na jam'iyyun adawa, Peter Obi da Atiku Abubakar, ba su da katabus.
Ya ce ba su da ishashshen goyon baya ta siyasa a Arewacin Najeriya da za ta ba su damar kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban ƙasa: 'Tinubu ya fitar da mara 'da kunya, ya kamata a saka masa a 2027'

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta kawo labarin cewa Ganduje ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka gudanar a Kano a karshen mako.
2027: Ganduje ya magantu kan tasirin Arewa
A ruwayar Daily Post, Ganduje ya ce Arewa ita ce ke da muhimmiyar rawa a duk lokacin da ake gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya, saboda yawan masu kada kuri'a da kuma tasirin yankin a siyasar kasar.
Ya ce duk da yana girmama 'yan adawa, Obi ko Atiku da ke da tsarin siyasa mai karfi da zai iya tattara kuri'un da ake bukata domin doke Tinubu a yankin Arewa.

Source: Twitter
A cewarsa:
"Arewa tana da matukar muhimmanci a duk wani zaben shugaban kasa a Najeriya. Da dukkan girmamawa ga abokanmu na jam'iyyun adawa, Peter Obi ko Atiku Abubakar da zai iya tattara isasshen goyon baya a wannan yanki domin kayar da Shugaba Tinubu a 2027."
Kiran Ganduje ga INEC
Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce duk da tattaunawar hadakar jam'iyyun adawa da ake yi a halin yanzu, har yanzu babu wata alamar da ke nuna cewa za su iya gina karfin da zai ba su damar samun gagarumar nasara a jihohin Arewa.
Ganduje ya kuma nuna damuwa kan karuwar yawan jam'iyyun siyasa a Najeriya, yana mai cewa hakan na iya rage ingancin tsarin dimokuradiyya idan ba a sanya tsauraran ka'idoji ba.
Saboda haka, ya bukaci hukumar zabe ta INEC da ta sake duba sharuddan rajistar jam'iyyun siyasa domin tabbatar da cewa jam'iyyun da za su shiga zabe suna da ingantaccen tsari, akida da kuma wakilci a fadin kasar.
Raddin Ganduje ga Atiku, El-Rufa'i
A baya, mun ruwaito cewa tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ce yunƙurin haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyun adawa da sunan tunkarar Bola Ahmed Tinubu a kakar zabe mai zuwa ba zai kai ko ina ba.
Dr. Ganduje wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya ke jagorancin jam'iyyar ya bayyana haka ne bayan ziyarar Sallah da shugabannin APC suka kai wa Buhari a gidansa da ke Kaduna lokacin yana raye.
Ganduje ya jaddada cewa APC tana da karfi kasancewar tana da gwamnoni 21 kuma za ta ci gaba da faɗaɗa tasirinta wurin kara jawo gwamnoni da sauran manyan yan siyasa masu fada a ji cikin gabanin 2027.
Asali: Legit.ng
