Osun: INEC Ta Sanar da Ranar Fara Rabon Katin Zaɓe, Ta Gargaɗi Masu Kada Ƙuri'a

Osun: INEC Ta Sanar da Ranar Fara Rabon Katin Zaɓe, Ta Gargaɗi Masu Kada Ƙuri'a

  • Hukumar INEC ta sanar da cewa za ta fara raba katin zaɓe (PVC) a faɗin jihar Osun gabanin zaɓen gwamna na 15 ga Agusta, 2025
  • Wadanda suka yi sabon rajista, suka sauya wurin rajista, suka nemi sabon kati ko suka sabunta bayanansu ne za su karɓi katin a wannan zagaye
  • INEC ta jaddada cewa mai katin ne kaɗai zai karɓi PVC ɗinsa, domin ba a amince da karɓa ta hannun wani ba kuma hakan laifi ne a doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun – Gabanin zaɓen gwamnan jihar Osun da za a gudanar ranar 15 ga Agustan 2026, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da cewa za ta fara raba katinan zaɓe.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta garzaya kotu bayan kuskuren tura sama da N5m wani asusu

Hukumar ta bayyana cewa za a fara rabon katin ne ga mazauna jihar a ranar Laraba, 22 ga watan Yulu, 2026 domin ba jama'a damar kada kuri'a.

INEC za ta fara raba katin zabe
Wasu katinan zaben yan Najeriya Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa sanarwar da Kwamishiniyar Hukumar INEC ta jihar Osun, Misis Oluwatoyin Babalola, ta fitar ta bayyana cewa rabon katinan ya shafi duk mutanen da suka yi rajistar zaɓe.

Wadanda INEC za ta ba katin zabe

Daily Post ta kawo labarin cewa waɗanda suka sauya wurin rajistarsu, masu neman maye gurbin katin da ya ɓace ko ya lalace, da kuma waɗanda suka sabunta bayanansu a lokacin rajistar masu kaɗa ƙuri'a da aka kammala kwanan nan.

A cewar Babalola, za a fara rabon katinan daga ranar 22 zuwa 28 ga Yulin 2026 a cibiyoyin rajista guda 332 da ke faɗin jihar Osun.

Ta ce za a riƙa gudanar da aikin daga 9.00 na safe zuwa 3.00 na rana a kowace rana, har da ranakun Asabar 25 ga watan Yuli da Lahadi 26 ga watan Yuli, 2026 domin bai wa masu kada ƙuri'a damar karɓar katunansu cikin sauƙi.

Kara karanta wannan

ADC: Abubakar Malami ya zabi abokin takarar gwamnan Kebbi a 2027

Hukumar INEC za ta ci gaba da aiki

Bayan kammala wannan mataki, INEC za ta ci gaba da rabon katinan a ofisoshinta na ƙananan hukumomi daga ranar 29 ga Yuli zuwa 7 ga Agusta, 2026. Hakanan za a riƙa gudanar da aikin tsakanin 9.00 na safe zuwa 3.00 na rana a kowace rana.

INEC ta ce kowa ya karbi katinsa da kansa
Shugaban INEC na kasa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Kwamishinar ta tunatar da al'umma cewa karɓar katin PVC dole ne ya kasance da kai tsaye, tana mai cewa ba a yarda wani ya karɓi wa wani katinsa ba.

Ta bayyana cewa duk wanda ya yi ƙoƙarin karɓar katin wani ya saɓawa dokar zaɓe, saboda haka INEC ba za ta miƙa wa wakili ko ɗan uwa katin wani mai rajista ba.

Babalola ta buƙaci duk wadanda suka cancanci kada ƙuri'a da su je su karɓi katin zaɓensu cikin wa'adin da aka tanada, tana mai jaddada cewa katin PVC ne kaɗai ake amincewa da shi wajen tantance masu kada ƙuri'a a ranar zaɓe.

Yan daba sun bude wuta a Osun

Kara karanta wannan

Buba Galadima: "Akwai kalubale kan tikitin Obi da Kwankwaso"

A baya, kun samu labarin cewa wani mamban jam'iyyar APC mai suna Taofeek Mustapha ya samu raunuka bayan wasu da ake zargin 'yan daban siyasa ne sun harbe shi a yankin Oluode-Aranyin da ke jihar Osun.

Rahotanni sun ce maharan sun isa wurin ne cikin wata mota kirar Toyota Sienna mai ruwan kasa ba tare da lambar rajista ba, inda suka fara harbe-harbe, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici.

Wani mazaunin yankin, Sola Hammed, ya ce mutane sun rika gudu suna neman mafaka domin tsira daga harsasan bindiga. Ya ce bayan harbe-harben ne suka ji wani yana neman taimako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng