ADC: Abubakar Malami Ya Zabi Abokin Takarar Gwamnan Kebbi a 2027

ADC: Abubakar Malami Ya Zabi Abokin Takarar Gwamnan Kebbi a 2027

  • Abubakar Malami ya zaɓi Musa Zagi a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamnan Kebbi na jam'iyyar ADC domin zaɓen 2027
  • Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa tana da kwarin gwiwar Zagi zai sauke nauyin da aka ɗaura masa idan suka samu nasara a zaɓe
  • Naɗin ya zo ne kwanaki bayan wata kotun tarayya ta ba da umarnin ƙwace kadarori 48 da ake dangantawa da tsohon AGF, Abubakar Malami

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Ɗan takarar gwamnan jam'iyyar ADC a Jihar Kebbi, Abubakar Malami, ya zaɓi Musa Zagi a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamna domin tunkarar zaɓen shekarar 2027.

Jam'iyyar ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaranta, Abubakar Atiku Musa, ya sanya wa hannu a ranar Juma'a, inda ya ce Malami ya amince da naɗin.

Kara karanta wannan

Dan takara zai soke abubuwan da suka shafi Tinubu idan ya ci zaben 2027

Abubakar Malami na jam'iyyar ADC
Abubakar Malami da ke yi wa ADC takara a Kebbi. Hoto: Abubakar Malami
Source: Twitter

Channels TV ta wallafa cewa sanarwar ta bayyana cewa jam'iyyar na da cikakken yaƙinin cewa Musa Zagi zai iya gudanar da ayyukan ofishin mataimakin gwamna yadda ya kamata idan ADC ta samu nasara a zaɓen 2027.

ADC ta yi kira ga magoya bayanta

Jam'iyyar ta kuma taya Musa Zagi murnar samun wannan dama tare da yi wa sauran 'yan takararta da ke neman mukamai daban-daban fatan alheri.

ADC ta buƙaci mambobinta da magoya bayanta su ci gaba da haɗin kai da jajircewa domin tabbatar da nasarar jam'iyyar a zaɓe.

Har ila yau, sanarwar ta yi kira ga a gudanar da zaɓe cikin lumana, adalci da gaskiya, tare da roƙon al'ummar Jihar Kebbi su fito su goyi bayan 'yan takarar jam'iyyar a rumfunan zaɓe.

Abuabakar Malami yana jawabi
Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami. Hoto: Abubakar Malami
Source: Facebook

Naɗin ya biyo bayan hukuncin kotu

Naɗin Musa Zagi ya zo ne bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin ƙwace kadarori 48 da ake dangantawa da Abubakar Malami, tsohon Babban Lauyan Tarayya (AGF).

Kara karanta wannan

Bauchi: Bala Mohammed ya yi garambawul a majalisar zartarwa, ya sauke kwamishinoni 2

The Cabble ta rahoto cewa mai shari'a Joyce Abdulmalik ta yanke hukuncin cewa Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa kadarorin sun samo asali ne daga wasu ayyukan da ake zargin ba su bi doka ba.

Kotun ta kuma ce Malami ya kasa gabatar da hujjojin da ke nuna cewa ya mallaki kadarorin ta hanyar halal, bayan da ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafe da buƙatun da shi da iyalansa da wasu kamfanoni suka gabatar.

M.A Abubakar ya zaɓi mataimaki

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC a Jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar ya zaɓi tsohon kwamishina, Farouk Mustapha, a matsayin mataimakinsa domin zaɓen 2027.

Sakataren Tsare-tsare na APC a jihar, Sallah Kafi, ya ce shugabannin jam'iyyar sun riga sun miƙa sunan da bayanan Mustapha a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamna.

Mustapha ya yi murabus daga mukaminsa tare da wasu kwamishinoni bayan Gwamna Bala Mohammed ya umarci duk masu riƙe da muƙaman siyasa masu son tsayawa takara da su ajiye mukamansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng