Magana Ta Fito: Dalilin da Ya Sa Tinubu Ya Ki zuwa Amurka, Ya Tura Shettima Taron UNGA

Magana Ta Fito: Dalilin da Ya Sa Tinubu Ya Ki zuwa Amurka, Ya Tura Shettima Taron UNGA

  • Mohammed Idris ya bayyana dalilin da ya sa Shugaba Bola Tinubu ya tura mataimakinsa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa UNGA
  • Ministan ya ce Shettima yana ɗauke da cikakken ikon wakiltar Tinubu da Jamhuriyar Tarayyar Najeriya a taron na Majalisar Ɗinkin Duniya
  • Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya tare da halartar tarurrukan manyan shugabanni da ganawar ƙasashen biyu a New York

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci Kashim Shettima ya wakilce shi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81, UNGA, saboda shugaban yana hutu na shekara-shekara.

Mohammed Idris ya ce Shettima yana ɗauke da cikakken ikon Shugaban Ƙasa da na Jamhuriyar Tarayyar Najeriya, yana mai watsi da ra’ayoyin cewa rashin Tinubu a taron zai rage martabar Najeriya a fagen diflomasiyya.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Tinubu ya aika saƙo da aka sanar da rasuwar tsohon gwamna a Najeriya

Shettima zai wakilci Tinubu a Amurka
Kashim Shettima na gaisawa da Shugaba Bola Tinubu Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Tinubu yana hutu na shekara-shekara

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ministan ya fitar ranar Litinin, 21 ga watan Satumban 2026 a shafinsa na X.

“Shugaba Tinubu yana hutu na shekara-shekara a halin yanzu, kuma shawarar da ya yanke na tura Mataimakin Shugaban Ƙasa ya jagoranci tawagar Najeriya ba sabon abu ba ne, kuma ba ta rage martabar ƙasar a fagen diflomasiyya.”

Tinubu ya umarci Shettima ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron UNGA na 81 da ake gudanarwa a New York.

A yayin taron, ana sa ran Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya tare da halartar tarurrukan manyan shugabanni da gudanar da ganawar ƙasashen biyu.

Shettima na ɗauke da cikakken ikon Najeriya

“Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima yana ɗauke da cikakken ikon Shugaban Ƙasa da Jamhuriyar Tarayyar Najeriya.” In ji shi

Ya bayyana cewa ganawar da Shettima zai gudanar a New York za ta taimaka wajen ciyar da muradun Najeriya gaba a fannoni da suka haɗa da zaman lafiya da tsaro, bunƙasar tattalin arziki, yaƙi da sauyin yanayi da kuma gyaran tsarin kuɗaɗen duniya.

Kara karanta wannan

Ta tabbata Tinubu ba zai je Amurka ba, ya ba Shettima umarni kan taron UNGA

Sauran abubuwan da za a tattauna sun haɗa da ci gaba mai ɗorewa da ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen duniya.

"Saboda haka, Najeriya za ta samu cikakkiyar wakilci mai inganci a duk tsawon babban taron.”

Rashin Tinubu ya jawo ce-ce-ku-ce

Sanarwar ministan ta zo ne a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan rashin Shugaba Tinubu a taron shekara-shekara da shugabannin ƙasashen duniya ke halarta.

A watan Yuli, jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce Tinubu zai halarci taron UNGA na 81 da kansa.

An kuma ruwaito cewa an shirya wa Tinubu zama kusa da Shugaban Amurka Donald Trump yayin taron.

Tinubu dai ya bar Abuja ranar 30 ga Agusta domin yin hutun makonni uku a Turai, inda Landan ya kasance wurin yada zangonsa na farko kafin ya wuce Faransa.

Daga bisani, Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar da cewa Tinubu zai koma Najeriya bayan kammala hutunsa, lamarin da ya haifar da hasashen ko zai halarci taron UNGA da kansa ko a’a.

Kara karanta wannan

Shettima ya yi magana da aka fahimci kalamansa a baibai kan Tinubu

Tinubu ba zai je UNGA ba
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ma'aikata sun rubuta wasika ga Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ma’aikatan gwamnati da ke ƙarƙashin ɓangaren ƙungiyar ƙwadago ta JNPSNC sun rubuta wasika zuwa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ma'aikatan sun buƙaci Shugaba Tinubu ya yi gaggawar kawo dauki domin magance tsananin matsin tattalin arzikin da ke addabar ma’aikata da waɗanda suke dogaro da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng