Kiristoci Sun Taso Gwamna Bago a Gaba, Ana Neman ba Kirista Mataimakin Gwamna

Kiristoci Sun Taso Gwamna Bago a Gaba, Ana Neman ba Kirista Mataimakin Gwamna

  • Kungiyar Kiristoci ta CZCCS a Niger ta bukaci APC da Gwamna Mohammed Bago su tsayar da Kirista a matsayin mataimakin gwamna
  • Kungiyar ta ce Kiristoci sun kai kusan kashi 45 cikin 100 na al'ummar Niger saboda haka sun cancanci a ba su kujerar mataimakin gwamna
  • Shugabannin kungiyar sun gargadi APC cewa idan ba a zabi Kirista a matsayin mataimakin gwamna ba, Kiristoci na iya komawa wasu jam'iyyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Kungiyar Coalition of Concerned Christian Stakeholders (CCCS) ta bukaci adalci a kujerar mataimakin gwamna a Niger.

Kungiyar ta bukaci jam'iyyar APC a Niger ta tsayar da Kirista a matsayin mataimakin gwamna a zaben shekarar 2027.

An bukaci Gwamna Bago ya ba Kirista mataimakin gwamna
Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Niger. Hoto: Mohammed Umaru Bago.
Source: Twitter

Kiristoci na neman kujerar mataimakin gwamnan Niger

A yayin taron manema labarai da aka gudanar a Minna, kungiyar ta ce Kiristoci sun kai sama da kashi 45 cikin 100 na al'ummar Niger, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Abba Kabir da gwamnonin APC da ke neman tazarce sun fadi matsayarsu kan Tinubu

Kungiyar ta bayyana cewa ba za ta amince da sake gabatar da tikitin Musulmi da Musulmi ba a wa'adin mulki na biyu na Gwamna Mohammed Bago.

Saboda haka, ta yi imanin cewa sun cancanci a ba su kujerar mataimakin gwamna domin tabbatar da adalci da daidaito.

Kungiyar ta ce tana adawa da abin da ta kira ci gaba da mayar da Kiristoci saniyar ware duk da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar.

Ta kuma yi zargin cewa wasu fitattun 'yan siyasar Kirista sun janye daga takara a zaben fidda gwani na APC saboda addininsu.

Sakataren kungiyar, Jude Johnson, ya ce sun yi shiru kan irin wannan matsala a gwamnatin baya da kuma lokacin zaben 2023, amma ba za su sake amincewa da hakan ba.

Ya ce tikitin Musulmi da Musulmi ba ya nuna mutunta bambancin addinai da ke akwai a jihar.

Kiristoci sun fara magana kan kujerar mataimakin gwamna a Niger
Taswirar jihar Niger da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Johnson ya ce akwai kwararrun 'yan APC Kirista daga yankin Sanatan Neja ta Gabas (Zone B) da suka cancanci zama mataimakin gwamna.

Ya kara da cewa tunda mafi yawan Kiristocin jihar suna wannan yanki, ya dace jam'iyyar ta zabo mataimakin gwamna daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Kujerun manyan jami'an Tinubu na rawa, ana kira a kore su

Ya kuma bayyana cewa Kiristoci sun mara wa Mohammed Bago baya a zaben 2023, saboda haka yanzu suna bukatar tikitin APC ya nuna adalci, daidaito da kuma bai wa kowa dama ta hanyar zabar Kirista a matsayin mataimakin gwamna.

Kungiyar ta yi gargadin cewa idan APC ba ta tsayar da Kirista a matsayin mataimakin gwamna ba, hakan na iya sa Kiristoci su koma wasu jam'iyyun siyasa da za su ba su damar samun wakilci mafi kyau.

Shugaban kungiyar, Jonathan Vatsa, ya bayyana cewa ya fuskanci barazana saboda kiraye-kirayen da yake yi ga gwamna da ya zabi Kirista a matsayin abokin takararsa. .

Vatsa ya kara da cewa sake gabatar da tikitin Musulmi da Musulmi kuskure ne a siyasance.

Ya ce idan jam'iyyun adawa suka gabatar da zabin da ya fi dacewa da bukatun Kiristoci, da dama daga cikinsu za su iya marawa wannan zabi baya.

A cewarsa, kasancewar Kiristoci sun kai kusan kashi 45 cikin 100 na al'ummar jihar Neja, suna da cikakken hakkin neman a ba su kujerar mataimakin gwamna domin tabbatar da adalci da wakilci.

Musulmai sun bukaci kujerar mataimakin gwamna

An ji cewa kungiyar Musulmi a jihar Oyo ta kosa da kalar mulkin da ake yi musamman duba da mabambantan addinai da ake da su a jihar Musulmin sun bukaci.

Kara karanta wannan

Majalisa na neman taka wa Tinubu birki kan tubabbun yan ta'adda a Najeriya

Gwamna Seyi Makinde ya nuna adalci da daidaito ta hanyar mara wa dan takarar Musulmi baya a zaben gwamnan PDP.

Kungiyar ta tuna yadda gwamnan ya nuna kusanci da Musulmi a baya, ciki har da gina masallaci da taimaka wa masu a zuwa Hajji da Umrah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.