Gwamnatin Neja Ta Kakaba Dokar Hana Fita, an Ji Dalili
- An samu barkewar rikicin kabilanci tsakanin al'ummar Fulani da na Kamuku a jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
- Rikicin kabilancin ya yi sanadiyyar hallaka rayukan mutane kusan 100 tare da jawo asarar dukiya mai tarin yawa
- Gwamnatin jihar Neja ta dauki matakin sanya dokar hana fita a garuruwan da lamarin ya shafa domin ganin an dawo da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - Gwamnatin jihar Neja karkashin jagorancin Gwamna Umaru Bago ta sanya dokar hana fita a wasu garuruwa da ke cikin karamar hukumar Rafi.
Gwamnatin ta sanya dokar hana fitar ne biyo bayan barkewar sabon rikicin kabilanci da ya lakume rayuka da dukiyoyi.

Source: Twitter
Gwamna Umaru Bago na Jihar Neja ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da ya kai ga al'ummomin da rikicin ya shafa tsakanin Kamuku da Fulani a Tashar Bako.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya nuna damuwa kan gargadin da Majalisar ɗinkin duniya ta yi wa Arewacin Najeriya
Gwamna Bago ya ba hukumomin tsaro umarni
Ya umarci hukumomin tsaro da su tura dukkan kayayyakin aiki da ake da su zuwa al'ummomin a matsayin wani bangare na kokarin dawo da zaman lafiya da kuma hana sake barkewar rushewar doka da oda, rahoton Premium Times ya tabbatar da hakan.
Ana iya tunawa cewa rikicin kabilancin ya samo asali ne daga takaddamar gona kuma ya zuwa yanzu ya lakume rayukan mutane kusan 80.
Bago, wanda mataimakinsa, Yakubu Garba ya wakilta, ya umarci hukumomin tsaro da su yi amfani da dukkan tsarin tsaro da ke akwai a fadin yankunan da abin ya shafa.
Ya kuma umarce su da su dauki matakan karfi da kuma na lumana domin shawo kan rikicin da kuma hana shi bazuwa.
Ya ziyarci wuraren da ake rikici
Gwamnan, wanda ya duba al'ummomin da abin ya shafa tare da gano wuraren da suka fi fuskantar hadari, ya ce binciken farko ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga takaddama a kan filin noma.

Kara karanta wannan
Hadimin Abba ya nanata zargin da ake yi wa Abdusalam Gwarzo na yin kwana da N308m
Ya umarci Sarkin Kagara, Alhaji Ahmad Garba-Gunna, da ya kafa Kwamitin zaman lafiya domin saukaka tattaunawa, gina amana, da kuma inganta zaman lafiya mai dorewa a tsakanin al'ummomin da abin ya shafa.

Source: Original
Bago ya kuma yi kira ga masu amfani da dandalolin sada zumunta da masu fada a ji da su guji yada bayanai masu tunzura mutane ko wadanda ba a tantance ba, wadanda ke da ikon dagula lamarin tsaro.
Ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnatin jihar za ta aiwatar da matakai na hana sake aukuwar rikicin, kuma ya bukaci al'ummomin da ke gaba da juna da su rungumi zaman lafiya.
'Yan bindiga sun kona makarantu a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa ‘yan bindiga sun ƙone fiye da ƙauyuka da garuruwa bakwai a kananan hukumomin Agwara da Borgu na jihar Neja.
Hakazalika, hare-haren hatsabiban sun jawo mutane da dama daga yankin ke ci gaba da zama a hannun masu garkuwa da mutane.
Wasu daga cikin wuraren da abin ya shafa da suka haɗa da Konkoso, Kasuwan Daji, Pissa, Gangale, Woro, Tungan Makeri, Old Gangale, Boiya, Bakinba da Wawa.
Asali: Legit.ng