Kanin Sarkin Dubai Ya Rasu, za a Yi Kwana 10 ana Zaman Makoki
- Ahmed bin Rashid Al Maktoum, ƙani ga firaministan UAE kuma mai mulkin Dubai, ya rasu yana da shekaru 76 a duniya
- Hukumomin Dubai sun sanar da kwana 10 na makoki a hukumance, tare da saukar da tutoci kasa a fadin masarautar saboda jimami
- Shugaban ƙasar UAE da mai mulkin Dubai sun mika saƙon ta'aziyya tare da yabawa gudunmawar da marigayin ya ba wa ci gaban ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Dubai – Hukumomin masarautar Dubai sun ayyana kwana 10 na makoki a hukumance biyo bayan rasuwar Sheikh Ahmed bin Rashid Al Maktoum, ƙani ga firaministan ƙasar UAE kuma mai mulkin Dubai, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum.
Sheikh Ahmed ya rasu ne yana da shekaru 76 a duniya, kamar yadda hukumomin masarautar suka sanar.

Source: Twitter
The Independent ta rahoto cewa sakamakon wannan rashi, za a rage tsawon tutocin ƙasar a duk faɗin masarautar a tsawon kwanakin makokin domin karrama marigayin.
Ana jimami a kasar Dubai
Mohammed bin Rashid Al Maktoum, wanda shi ne mataimakin shugaban ƙasa kuma firaministan UAE, ya nuna alhininsa kan rasuwar ɗan uwan nasa ta hanyar wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
Ya rubuta cewa:
"Allah ya yi wa Sheikh Ahmed bin Rashid Al Maktoum rahama. Allah ya yi muku rahama, ɗan uwana. Ba ka gaban idanuwanmu amma ba ka rabu da addu'o'inmu da ƙalokanmu ba, ya Ahmed. Allah ya sadar da kai faffadan gidansa na Aljanna, ya kuma ba mu da na kusa da kai haƙurin jure rashinka."
Dudunmawar marigayin a Dubai
Accord News ta ruwaito cewa shugaban ƙasar UAE, Mohamed bin Zayed Al Nahyan, shi ma ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga mai mulkin Dubai kan wannan rashi.
Ya kwatanta gudunmawar da Sheikh Ahmed ya ba wa ci gaban UAE tun lokacin kafa ƙasar a matsayin mai tarin yawa, yana mai cewa aikinsa zai ci gaba da kasancewa tubali na samun nasarar al'umma.
"Muna alhinin wannan rashi kuma muna tuna irin gudunmawar da ya bayar wajen gina wannan ƙasa."
Sheikh Ahmed shi ne ɗa na huɗu kuma mafi ƙaranci a wurin marigayi Sheikh Rashid bin Saeed Al Maktoum, tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma mai mulkin Dubai wanda ke ɗaya daga cikin ginshiƙan kafa masarautar.

Source: AFP
A tsawon rayuwarsa, ya riƙe muƙamai daban-daban a fannin tsaro, wasanni, da kasuwancin gidaje a Dubai.
Shi ne shugaban fannin 'yan sanda da tsaron jama'a na Dubai, kuma ya taka rawa sosai a harkar tsere da kiwon dawaki na masarautar.
Ladanin Makkah ya rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Ladanin Masallacin Harami na Makkah, Sheikh Ibrahim bin Adel Hamza Al-Madani, ya rigamu gidan gaskiya.
An fitar da sanarwar mutuwar tasa ne a yau a wata kafar Saudiyya da aka sani da kawo rahotannin abubuwan da ke faruwa a masallatai masu alfarma guda biyu.
Rasuwar Al-Madani ta faru ne bayan ya gudanar da abin da aka ruwaito a matsayin kiran sallarsa na ƙarshe a Masallacin Harami a ranar Litinin, 11 ga watan Rabi Al-Awwal 1448 AH.
Asali: Legit.ng
