Dickson: Jagoran NDC na Kasa Ya Fadi Dalilin Kin Shiga APC, Ya Aika Sako ga Kwankwaso da Obi

Dickson: Jagoran NDC na Kasa Ya Fadi Dalilin Kin Shiga APC, Ya Aika Sako ga Kwankwaso da Obi

  • Sanata Seriake Dickson ya bayyana dalilin da sanya ya ƙi shiga jam'iyyar APC mai mulki bayan ya fice daga PDP
  • Tsohon gwamnan na Bayelsa ya ce an kafa NDC ne domin samar da wani zabin siyasa na daban da ƙarfafa tsarin jam’iyyu da dama
  • Dickson ya yaba wa Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, tare da kira ga ’yan NDC su manta da sabanin zaɓen fidda gwani na ’yan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Seriake Dickson, jagoran ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), ya fito ya bayyana dalilinsa na kin shiga jam'iyyar APC mai mulki.

Sanata Seriake Dickson ya ce ya ƙi shiga APC ne saboda bai yarda Najeriya ta koma ƙasar da jam’iyya ɗaya ke mulki ba.

Kara karanta wannan

Tirkashi: ADC ta bankado makarkashiyar da ake kullawa a Arewa gabanin zaben 2027

Dickson ya yi magana kan NDC
Peter Obi, Sanata Henry Seriake Dickson tare da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: IamHSDickson
Source: Twitter

Dickson ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Alhamis, 17 ga watan Satumban 2026 lokacin da aka karamma shi da lambar yabo.

Ya yi magana nelokacin da shugabannin jaridar Leadership, Mike Okpere, suka kai masa sanarwar karramawar gwarzon dan siyasar shekarar 2026 na Leadership.

Dickson bai son tsarin jam'iyya 1

Da yake magana kan abubuwan da suka haifar da kafa NDC, Dickson ya ce an samar da jam’iyyar ne a wani lokaci mai wahala, lokacin da mutane kalilan suka yi imanin cewa sabuwar jam’iyya za ta iya samun ƙarfi.

Tsohon gwamnan Bayelsa ya ce bayan abin da ya bayyana a matsayin raguwar tasirin tsohuwar jam’iyyarsa, Peoples Democratic Party (PDP), ya yanke shawarar kada ya shiga APC.

“Ban yarda cewa ya kamata Najeriya ta zama ƙasar da jam’iyya ɗaya ke mulki ba,” in ji Dickson.

Ya ce maimakon ya koma wata tsohuwar jam’iyyar siyasa, ya zaɓi kafa NDC domin samar wa ’yan Najeriya wani sabon dandali da kuma taimakawa wajen ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyyar jam’iyyu da dama.

Kara karanta wannan

Tun ba a je ko'ina ba shirin hada kan 'yan adawa don tunkarar Tinubu ya gamu da cikas

“Mun gina babbar jam’iyyar adawa”

Dickson ya ce cikin ’yan watanni bayan kafa NDC, jam’iyyar ta samu ci gaba tare da zama wata muhimmiyar kafa a siyasar adawa a Najeriya.

“Bayan watanni, mun gina jam’iyya mai ƙarfi da kuma babbar jam’iyyar adawa a Najeriya,” in ji shi.

Ya gode wa ’yan Najeriya, shugabannin NDC, jami’anta, mambobinta da magoya bayanta bisa amincewa, jajircewa da sadaukarwar da suka nuna wajen gina jam’iyyar.

Dickson ya kuma yaba wa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, da Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, bisa haɗin gwiwar da suka bayar a wannan tafiya ta siyasa.

Wane kira Dickson ya yi ga 'yan NDC?

Yayin da NDC ta kammala zaɓen ’yan takararta domin babban zaɓen 2027, Dickson ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da su ajiye duk wani saɓani da ya taso sakamakon tsarin zaɓen ’yan takara.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi maganar sayen hannun jari a matatar Dangote, ya ba 'yan Najeriya shawara

Ya bukaci mambobin jam’iyyar su mayar da hankali kan tattara goyon bayan jama’a ga dukkan ’yan takaranta tare da ƙara ƙarfafa NDC a matsayin babbar jam’iyyar adawa.

Dickson ya fadi dalilin kin shiga APC
Sanata Dickson na jawabi a wajen taron NDC Hoto: @IamHSDickson
Source: Facebook

Kwankwaso ya ziyarci Sanata Dickson

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata tawaga a ƙarƙashin jagorancin shugaban Kwankwasiyya na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ta ziyarci jagoran NDC na kasa, Henry Seriake Dickson.

Bangarorin biyu sun shiga wani taron sirri domin nemo mafita ga rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng