Yan Adawa Sun Yi wa Gwamnati Ca da Ta Ce Ƴan Ta'adda Sun Yi Kuste cikin Jami'an Tsaro
- Jam'iyyun adawa sun yi martani bayan Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa an samu wasu yan ta'adda sun yi wa jami'an tsaro kutse
- Hadimin Bola Tinubu, Daniel Bwala ya ce Fadar akwai yiwuwar wasu masu alaka da 'yan ta'adda sun kutsa cikin hukumomin tsaro
- Lamarin ya sa yan adawa da suka hada da NDC, ADC da wasu jam'iyyu sun harzuka da yadda su ka ce ya nuna gazawar gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT AbuJa – Jam'iyyun adawa a Najeriya sun soki gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bayan Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa akwai yiwuwar wasu masu alaka da kungiyoyin ta'addanci sun kutsa cikin hukumomin tsaron kasar.
Jam'iyyun SDP, ADC, YPP, PDP da NDC sun bayyana cewa wannan furuci ya kara tabbatar da gazawar gwamnatin tarayya wajen shawo kan matsalar tsaro da ke ci gaba da addabar Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa sun kuma bukaci a gudanar da bincike mai zurfi tare da hukunta duk wani jami'in tsaro da aka samu yana hada kai da 'yan ta'adda.
Fadar shugaban kasa ta magantu kan tsaro
Daily Post ta wallafa cewa hadimin shugaban kasa shawara, Daniel Bwala, ne ya bayyana cewa akwai yiwuwar kitsen yayin wata tattaunawa, inda ya ce gwamnati ta riga ta dauki wasu matakan dakile barazanar.
Furucin na Bwala ya zo ne bayan rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun yi ikirarin cewa wani soja a jihar Yobe ya bace na wasu kwanaki kafin daga baya aka ce an gan shi tare da mayakan Boko Haram yayin wani hari.
Rahotannin sun kuma yi zargin cewa an kama shi daga baya tare da gano wasu bayanai da suka kai ga cafke wasu jami'an tsaro. Sai dai babu wata hukuma da ta tabbatar da wadannan ikirari.
Da yake karin haske, Bwala ya ce ba Najeriya kadai ke fuskantar irin wannan kalubale ba, yana mai cewa kasashe da dama sun taba samun irin wannan matsala.
Tsaro: Abin da jam'iyyun adawa su ka ce
Sai dai jam'iyyun adawa sun ce wannan bayani ya kamata ya biyo bayan bincike da gurfanar da masu laifi a gaban kotu, ba wai furuci kadai ba.
Kakakin SDP, Rufus Aiyenigba, ya ce babban nauyin tabbatar da tsaro yana kan shugaban kasa a matsayinsa na babban kwamandan rundunonin soji, yana mai cewa gwamnati ta gaza cika wannan muhimmin nauyi.

Source: Twitter
Hakazalika, kakakin NDC, Osa Director, ya ce kalaman Bwala sun nuna gazawar gwamnatin APC wajen magance matsalar tsaro tun bayan hawanta mulki.
Shi ma kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya tambayi dalilin da ya sa ba a gurfanar da kowa ba idan har gwamnati na da sahihan hujjojin kutsen 'yan ta'adda cikin hukumomin tsaro.
Rashin tsaro: Yan bindiga sun yi ta'asa
A wani labarin, kun ji cewa Akalla mutum 13 sun rasa rayukansu a hare-haren da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto duk da an samu agajin jami'an tsaro.
Dakarun tsaro da 'yan sa-kai sun dakile yunƙurin mamaye Unguwan Lalle bayan fafatawar sa'o'i da dama, bayan sun gaza a Unguwan Lalle, maharan sun kashe mutum shida a Mazau, huɗu a Turtsawa da uku a Tsamaye.
Ƙoƙarin jin ta bakin 'yan majalisar dokokin jihar Sokoto masu wakiltar Sabon Birni, Hon. Aminu Boza da Hon. Sa'idu Ibrahim, bai yi nasara ba saboda ba su amsa kiran wayarsu ba a lokacin hada labarin.
Asali: Legit.ng


