Matsala Ta Fara daga Gida, Jigon APC Ya Ce Kiristoci ba Za Su Yi Muslim/Muslim ba

Matsala Ta Fara daga Gida, Jigon APC Ya Ce Kiristoci ba Za Su Yi Muslim/Muslim ba

  • Wani jigon APC a Niger ya yi kaca-kaca da matakin Bola Tinubu na daukar mataimakinsa a zaben 2027
  • Jonathan Vatsa, ya ce tikitin Musulmi da Musulmi ba zai samu karɓuwa daga Kiristoci ba a zaɓen 2027
  • Vatsa ya bayyana cewa maimaita tikitin Musulmi da Musulmi cin fuska ne ga Kiristocin Najeriya inda ya ce za a samu matsala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Wani jigon jam'iyyar APC a Niger, Jonathan Vatsa, ya soki matakin Shugaba Bola Tinubu na daukar mataimakinsa.

Vatsa ya ce sake zaɓar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa zai jawo masa matsala.

Jigon APC ya ce Muslim/Muslim cin fuska ne ga Kiristoci
Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima.
Source: UGC

Vatsa ya bayyana hakan ne sa'o'i kaɗan bayan sanar da Shettima, yana mai cewa tikitin Musulmi da Musulmi ba zai samu karɓuwa ba a zaɓen 2027, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Martanin El Rufa'i ga ICPC kan zargin ganawar siyasa a asibiti

'Muslim/Muslim cin fuska ne ga Kiristoci' - Jigon APC

Ya ce maimaita tsarin da aka yi a zaɓen 2023 cin fuska ne ga al'ummar Kiristoci a Najeriya, kuma hakan ya nuna rashin kula da damuwarsu.

Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai, Al'adu da Yawon Buɗe Ido ya ce duk wanda ya ba shugaban ƙasa wannan shawara bai yi masa alheri ba.

A cewarsa, yanayin siyasar Najeriya ya sauya idan aka kwatanta da shekarar 2023, saboda haka bai kamata a maimaita irin wannan tsari ba.

Ya ƙara da cewa zarge-zargen da ake yi game da kashe Kiristoci a Najeriya sun sa maimaita tikitin Musulmi da Musulmi zai ƙara jawo cece-kuce.

Vatsa ya ce zai yi matuƙar wahala a shawo kan Kiristoci su zaɓi APC idan sauran jam'iyyu suka tsayar da 'yan takara Kirista.

Ya tambaya irin saƙon da mambobin APC Kirista za su kai wa al'ummarsu domin su goyi bayan wani tikitin Musulmi da Musulmi.

Daukar Kashim Shettima ya fara jawo matsala
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Facebook

Vatsa ta tunatar cewa kwanan nan ya roƙi Gwamna Umar Mohammed Bago ya zaɓi Kirista a matsayin mataimakinsa domin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Kotu ta ci tarar dan takarar gwamna a ADC miliyoyi kan fastocin siyasa a Adamawa

Ya kwatanta halin da Kiristoci ke ciki da karin maganar Littafi Mai Tsarki game da dutsen da magina suka ƙi amma daga baya ya zama muhimmi.

A cewarsa, sake tsayar da tikitin Musulmi da Musulmi ba abin karɓa ba ne, kuma zai haifar da babban ƙalubale ga Shugaba Tinubu.

Ya ce sai dai idan shugaban ƙasa yana da wata dabara ta daban wajen cin zaɓe, wannan mataki zai iya haifar masa da sakamako mai tsanani.

Vatsa ya ce Kiristoci da dama suna jin rashin tsaro, saboda haka za su fi samun kwanciyar hankali idan mataimakin shugaban ƙasa Kirista ne.

Ya kuma ce ƙasashen duniya na sa ido kan yadda siyasar Najeriya za ta kasance a 2027, musamman dangane da matsayin Kiristoci.

A ƙarshe, ya ce ba ya adawa da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ko al'ummar Musulmi, sai dai yana neman adalci, daidaito da gaskiya a tsarin siyasar Najeriya.

Kiristocin Arewa sun magantu kan daukar Kashim

An ji cewa wata kungiyar Kiristoci a yankin Arewacin Najeriya ta bayyana matsayarta kan sake daukar Kashim Shettima a matsayin mataimaki.

Kara karanta wannan

'Kar mu ji, kar mu gani': Atiku ya gargadi gwamnati game da Obi, El Rufa'i

Shugaban kungiyar, Fasto Jolly Usman, ya ce ƙwarewar Shettima da haɗin gwiwarsa da Tinubu sun taimaka wajen inganta tsaro.

Ƙungiyar ta bukaci 'yan Najeriya su yi hukunci kan shugabanni bisa ayyukansu da nagartarsu, ba wai la'akari da bambancin addini kaɗai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.