‘Hanyar da Atiku Zai Kayar da Tinubu cikin Sauki a Zaben Shekarar 2027’
- Wata ƙungiyar siyasa ta bukaci jam'iyyar ADC ta zaɓi ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa da ke da karɓuwa
- Ƙungiyar ta ce zaɓin kwararren mataimakin shugaban ƙasa, mai farin jini da goyon bayan jama'a zai taimaka wa ADC
- Ta kuma buƙaci shugabannin ADC su fifita haɗin kai, maslahar ƙasa da gina ƙawance tsakanin yankuna domin ƙara samun goyon baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ƙungiyar Southern Political Progressives Amalgamation Forum ta ba jam'iyyar ADC shawara game da zaben 2027.
Kungiyar ta buƙaci jam'iyyar ADC da ta yi taka-tsantsan wajen zaɓen ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa kafin zaɓen 2027.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da Kwamared Anga Fidelis, Eniafe Ayomide da Johnson Iheanacho suka sanya wa hannu, cewar The Guardian.
'Abin da zai iya ba ADC nasara a zabe'
Ta ce wannan mataki zai iya taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa damar jam'iyyar a fafatawa da APC.
Kungiyar ta ce ya dace ADC ta zaɓi wanda yake da karɓuwa a faɗin Kudancin Najeriya, tare da kwarewar siyasa da farin jini a tsakanin al'umma.
Ta yi wannan bayani ne bayan rahotannin da suka danganta tsohon ministan sufuri kuma tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi, da kujerar mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa tare da Alhaji Atiku Abubakar.
A cewar ƙungiyar, ya kamata ADC ta rungumi dabarar da za ta ƙarfafa tushen goyon bayanta a dukkan shiyyoyin siyasa shida na Najeriya domin ƙara yuwuwar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa.
Ta bayyana cewa zaɓen mataimakin shugaban ƙasa ya kamata ya dogara da abubuwa kamar karɓuwa a ƙasa baki ɗaya, gogewar siyasa, goyon bayan jama'a da kuma ikon cike gurbin ɗan takarar shugaban ƙasa.
Sanarwar ta ce zaɓin mataimakin shugaban ƙasa muhimmiyar dabara ce da za ta iya tasiri kan sakamakon zaɓe.
Don haka, jam'iyyar ADC ta tabbatar wanda za a zaɓa yana da karɓuwa sosai kuma zai taimaka wajen samun nasarar jam'iyyar.

Source: Twitter
2027: Kungiya ta kawo shawara ga ADC
Ƙungiyar ta ƙara da cewa burin jam'iyyar ya kamata ya kasance gabatar da tikitin takara mai jan hankalin 'yan Najeriya da ke neman wata madadin jam'iyya a zaɓen shekarar 2027.
Har ila yau, ta shawarci shugabannin ADC su tabbatar cewa duk wasu matakan da za su ɗauka a cikin jam'iyyar za su ƙarfafa haɗin kai da kuma ƙara wa mambobi da magoya baya kwarin gwiwa, cewar Punch.
A cewar ƙungiyar, gina ƙawance mai faɗi tsakanin yankuna daban-daban da ƙungiyoyin masu ruwa da tsaki zai kasance muhimmin ginshiƙi idan ADC na son kalubalantar APC yadda ya kamata a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
Ta bayyana cewa idan aka yi kyakkyawan shiri, aka tabbatar da haɗin kai a cikin jam'iyyar kuma aka gabatar da tikitin takara mai karɓuwa, ADC za ta iya ƙara yuwuwar yin gogayya mai ƙarfi a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
A lokacin da aka wallafa rahoton, jam'iyyar ADC da kuma Rotimi Amaechi ba su fitar da wata sanarwa ko martani kan matsayar wannan ƙungiya ba.
ADC ta bukaci binciken lafiyar Tinubu
An ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta sake taso Bola Tinubu a gaba game da sake neman takara a 2027 ADC ta bukaci.
Majalisar Tarayya ta binciki ko Shugaba Bola Tinubu na da cikakkiyar lafiya da ikon gudanar da mulkin Najeriya.
Jam'iyyar ta danganta bukatar da rikicin shugabancin Hukumar BCDA, tana zargin wasu da ba a zaba ba na iya amfani da ikon shugaban kasa.
Asali: Legit.ng


