Sowore: Dan takara zai Soke Abubuwan da Suka Shafi Tinubu idan Ya Ci Zaben 2027

Sowore: Dan takara zai Soke Abubuwan da Suka Shafi Tinubu idan Ya Ci Zaben 2027

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya yi alƙawarin soke sunayen manyan hanyoyi da ma'aikatun gwamnati
  • Matakin da zai dauka zai shafi kadarorin ƙasa da aka raɗawa sunan shugaba Bola Tinubu da sauran jami'ai idan ya zama shugaban ƙasa a 2027
  • Sowore ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a ranar Juma'a, yayin da yake mayar da martani kan wani matakin gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya fara magana kan abubuwan da zai yi idan ya yi nasara a 2027.

Sowore ya sha alwashin soke raɗa wa manyan hanyoyi, ma'aikatun gwamnati da sauran kadarorin ƙasa sunayen shugaba Bola Tinubu da sauran jami'an gwamnati idan har aka zaɓe shi a zaben 2027.

Kara karanta wannan

An yi kicibis, sojoji sun yi ram da 'dan bindiga a hanyar sintiri

Bola Tinubu da Omoyele Sowore
Shugaba Bola Tinubu a hagu, Omoyele Sowore a dama. Hoto: Bayo Onanuga Omoyele Sowore
Source: Twitter

Matakin da Sowore zai dauka

Sowore ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Juma'a, biyo bayan matakin gwamnatin tarayya na sauya sunan babbar hanyar da ta haɗa Legas da Calabar zuwa sunan Tinubu.

Ya rubuta cewa:

"Sauya sunayen manyan hanyoyi, cibiyoyin ƙasa, da kadarorin gwamnati da aka raɗawa jami'an gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wadda ta jefa 'yan Najeriya cikin talauci da kuma wadanda suka taimaka wa durƙushewar ƙasar, zai zama babban alƙawari da za a cika cikin gaggawa a ƙarƙashin gwamnatin Sowore bayan 2027."

An sa wa hanya sunan Tinubu

Martanin nasa ya biyo bayan sanarwar da Ministan Ayyuka, David Umahi ya yi, inda ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta sauya sunan babbar hanyar Lagos-Calabar Coastal Highway zuwa Bola Ahmed Tinubu.

Punch ta ruwaito cewa Umahi ya fitar da sanarwar ne a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai a Abuja, inda ya ce an ɗauki matakin ne domin karrama hangen nesan da Tinubu yake da shi game da aikin.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: INEC na shirin yin zaben gwaji kafin siyasar 2027 a Najeriya

A cewar ministan, ma'aikatar ayyuka ta amince da sauya sunan ne bayan shawarwari da aka yi da shugabannin ma'aikatar.

"Wannan babbar hanya ta gabar teku an sanya mata sunan Bola Ahmed Tinubu.
"Dubi ga ikon da aka ba ni a matsayin Ministan Ayyuka, bayan tattaunawa da Babban Sakatare na,karamin ministan, daraktoci da ma'aikatan ma'aikatar, mun yanke shawarar sanya mata sunan Tinubu."
Bola Tinubu da jami'an gwamnati
Wata ma'aikatar gwamnati da aka radawa sunan Tinubu a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tsarin ilimin da Sowore zai yi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sowore ya yi alƙawarin soke hukumar shirya jarrabawar shiga jami'o'i (JAMB) da kuma soke shirin yi wa ƙasa hidima na matasa (NYSC) a yadda suke yanzu idan aka zaɓe shi.

Omoyele Sowore ya bayyana cewa ya kamata manyan makarantu su riƙa gudanar da tsarin daukar ɗalibai a ƙarƙashin tsari mai nuna gaskiya da cancanta.

Ya ce zai maye gurbin NYSC da tsarin samar da aikin yi na ƙasa na shekaru biyu na sa-kai wanda zai mayar da hankali kan aikin yi, kasuwanci da kuma dabarun dogaro da kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng