An Taso Tinubu a Gaba game da Lafiyarsa kan Sake Neman Takara a 2027
- Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta sake taso Bola Tinubu a gaba game da sake neman takara a 2027
- ADC ta bukaci Majalisar Tarayya ta binciki ko Shugaba Bola Tinubu na da cikakkiyar lafiya da ikon gudanar da mulkin Najeriya
- Jam'iyyar ta danganta bukatar da rikicin shugabancin Hukumar BCDA, tana zargin wasu da ba a zaba ba na iya amfani da ikon shugaban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta ba Majalisar Tarayyya shawara kan shugaban kasa, Bola Tinubu.
ADC ta bukaci Majalisar Tarayya ta yi amfani da tanade-tanaden kundin tsarin mulki domin tantance ko Shugaba Bola Tinubu har yanzu yana da koshin lafiya.

Source: Facebook
Mai magana da yawun jam'iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana wannan matsaya cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma'a, cewar Punch.
Zargin da ADC ke yi kan Bola Tinubu
Jam'iyyar ta ce hakan ya zama dole saboda tana zargin shugaban kasa ya rasa cikakken iko kan gwamnatin sa da tafiyar da harkokin mulki.
Har ila yau, ADC ta yi zargin cewa wasu mutane da ba a zabe su ba na iya amfani da ikon shugaban kasa.
Ta ce hakan na iya faruwa ba tare da cikakken sanin mutumin da 'yan Najeriya suka zaba domin jagorantar kasar ba.
Sanarwar ta biyo bayan cece-kucen da suka dabaibaye rikicin shugabanci a Hukumar Raya Al'ummomin Kan Iyaka, wato BCDA.
A cewar ADC, rahotannin da ke cewa wani jami'i da aka sanar da cire shi daga mukami har yanzu yana ci gaba da zama a ofis suna tayar da tambayoyi.

Source: Twitter
Shakkun da ADC ke da shi kan Tinubu
Jam'iyyar ta ce irin wannan lamari yana jefa shakku kan ikon shugaban kasa da kuma sahihancin yadda ake aiwatar da umarnin gwamnati.
Sanarwar ta ce idan rahotannin da suka shafi BCDA gaskiya ne, batun ya wuce rikicin mukami guda kawai, cewar Vanguard.
Ta ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne tambayar wanda ke rike da ragamar shugabancin Najeriya a zahiri.
ADC ta kara da cewa idan ana iya yin watsi da umarnin shugaban kasa kan nade ko cire mukami ba tare da wani sakamako ba.
Jam'iyyar ta ce hakan yana nuna ba rudanin gudanarwa kadai ake fuskanta ba, illa gwagwarmayar neman iko a fadar shugaban kasa.
Ta bayyana cewa rikicin BCDA ba shi ne kadai ba, domin akwai wasu abubuwa makamantansu da suka nuna rudani a gwamnatin Tinubu.
Jam'iyyar ta gargadi cewa rashin tabbas kan umarnin shugaban kasa na iya raunana hukumomi da kuma rage kwarin gwiwar masu zuba jari.
Saboda haka ta bukaci Majalisar Tarayya ta gudanar da aikinta na sa ido bisa tanadin kundin tsarin mulki ba tare da bata lokaci ba.
Ta ce majalisar ta tabbatar shugaban kasa yana da cikakkiyar lafiya ta jiki da hankali wajen gudanar da ayyukansa.
2027: Atiku ya bukaci Tinubu ya hakura
A wani labarin, an ji cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya sake ba Shugaba Bola Tinubu shawara game da zaben 2027.
Atiku ya ce rikicin shugabancin Hukumar BCDA da makamancinsa a NIPOST sun nuna gazawar gwamnati wajen aiwatar da doka.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ya kamata Tinubu ya mayar da hankali kan magance matsalolin Najeriya.
Asali: Legit.ng


