Baya Ta Haihu: Kotu Ta Umarci INEC Ta Sauya Sunan Dan Takarar APC Cikin Sa'o'i 48

Baya Ta Haihu: Kotu Ta Umarci INEC Ta Sauya Sunan Dan Takarar APC Cikin Sa'o'i 48

  • Rahotanni sun bayyana cewa babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ayyana Barrista Ghani Arobo a matsayin halastaccen ɗan takarar APC na mazaɓar Owo/Ose
  • Kotun ta bai wa INEC wa'adin sa'o'i 48 da ta saka sunan Arobo a shafin tantance ƴan takara bayan ta soke maye gurbinsa
  • Alƙalin kotun ya ce APC ta yi kuskure wajen sauya sunan wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani, tare da bayyana matakin a matsayin wanda bai dace da doka ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ayyana Barrista Ghani Arobo a matsayin halastaccen ɗan takarar jam'iyyar APC na mazaɓar Owo/Ose da ke jihar Ondo.

Kotun ta kuma umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta sanya sunan Arobo a shafin tantance ƴan takara cikin sa'o'i 48.

Kara karanta wannan

APC: Dan majalisar tarayya ya rasa tikitin takara, kotu ta sauya sunansa da wani

Amupitan a ofishin hukumar INEC
Shugaban INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Daily Trust ta rahoto cewa Mai shari'a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa Arobo ne ya lashe zaɓen fitar gwani na APC bisa ka'ida.

Dalilin da kotu ta yi hukuncin

A cewar kotun, APC ta yi kuskure wajen maye gurbin sunan Arobo da Emmanuel Adelegbe bayan zaɓen fitar da gwani.

Mai shari'a Lifu ya ce jam'iyyar ta kasa gabatar da sahihin rahoton sakamakon zaɓen fitar da gwani, yana mai bayyana hujjojin da APC ta gabatar a matsayin marasa daidaito kuma marasa inganci.

Ya kuma ce jam'iyyar APC ta zama "shaida mai rauni" a shari'ar saboda yadda ta gudanar da lamarin.

Sai dai kotun ta ce shaidun da Arobo da INEC suka gabatar sun kasance masu ƙarfi, daidaito kuma ba a iya rushe su ba, kasancewar INEC ta sa ido kan zaɓen fitar da gwanin.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa
Shugaban APC, Nentawe Yilwatda. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Martanin Arobo bayan hukuncin

Kara karanta wannan

A ba su wuta: Gwamnan Bauchi ya umarci sojoji a shafe 'yan bindiga

Bayan yanke hukuncin, Punch ta wallafa cewa Barrista Ghani Arobo ya yabawa ɓangaren shari'a bisa tabbatar da bin doka da adalci.

Ya kuma buƙaci INEC ta gaggauta aiwatar da umarnin kotun domin kauce wa duk wata matsala da za ta iya shafar shirye-shiryen zaɓe.

Arobo ya kuma roƙi APC, magoya bayanta da sauran masu ruwa da tsaki su mutunta hukuncin kotun tare da guje wa duk wani mataki da ka iya tayar da hankali.

PDP ta yi murna da matakin INEC

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɓangaren jam'iyyar PDP mai biyayya ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi murnar wallafa sunan Sanata Sandy Onor a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar.

Jam'iyyar ta ce matakin da INEC ta ɗauka ya kawo ƙarshen jita-jitar da ake yaɗawa cewa PDP ba za ta iya fitar da ɗan takara a zaɓen 2027 ba.

Shugabannin jam'iyyar sun bayyana wallafa sunan Onor da mataimakinsa Babangida Umar a matsayin babban ci gaba ga shirye-shiryensu na babban zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng