‘Kun Ce Ba Ku Son Tsoho’, Sule Lamido Ya Yi Watsi da Masu Kiran Ya Fito Takara

‘Kun Ce Ba Ku Son Tsoho’, Sule Lamido Ya Yi Watsi da Masu Kiran Ya Fito Takara

  • Sule Lamido bai gamsu da tsiraru masu zuga shi cewa ya nemi takarar shugaban kasa a Najeriya ba
  • Babban ‘dan siyasar ya ce idan har matasa sun ce ba su son tsofaffi, babu dalilin ya nemi takara
  • Alhaji Sule ya tuna wa Najeriya lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya hana tsofaffi rike mukami

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Jigawa - Sule Lamido ya ki daukar zugar da ake yi masa na tsaya wa takarar shugaban kasa a Najeriya a jam’iyyar PDP.

Alhaji Sule Lamido ya tuna wa ‘yan jarida yadda ake sukar tsofaffi musamman daga wajen matasa da suke ganin lokacinsa ne.

Sule Lamido
Sule Lamido lokacin yana minista, yana bayan Olusegun Obasanjo Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Sule Lamido zai nemi takarar shugaban kasa?

A wata hira da aka gani a Explorer Hausa, Sule Lamido ya yi watsi da kiraye-kirayen neman shugabancin Najeriya a 2027.

Kwararren ‘dan siyasar ya ce ko yana da sha’awar neman mulki, tunda matasa ba su kaunar tsofaffi, burin shi bai da wani amfani.

Kara karanta wannan

Pantami ya shirya wa 2027 da kyau, ya soma jefa wa APC maganganu a dunkule

An ji ya ce:

"Ko ina son takarar, ba ka so na, ya zan yi? Ko ina son takarar, kun ce ku ba ku yarda ba, kun ce na tsufa."

Da aka bukaci ya jarraba sa’arsa a filin zabe, tsohon gwamnan na Jigawa ya ce shi duk abin da zai yi, to da gaske ya yi.

"Kun ce ba ku son tsoho. Idan ban hakura ba, ya zan yi? Ka ce ba ka so na, me zan yi maka?

- Sule Lamido

Shi ma ‘dan jaridan da ya dage yana so ya ga irin Sule a fagen siyasa, sai ya fada masa cewa wannan ra’ayin shi ne kurum.

Bayan dubban mutanen da ba su tare da shi, ‘dan siyasar yana zargin an masa wannan magana ne saboda dai a faranta masa rai.

Sule Lamido yake cewa:

“Watakila don kana gaba na a yanzu, don ka ‘dan dadada mani rai na, saboda in ji dadi ko? Karya ka ke yi na gane ka.

Kara karanta wannan

Tsakani da Allah Peter Obi ba zai iya cin zabe ba in ji Sanatan NDC, Rufai Hanga

Sule.
Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido tare da mai gidansa Shugaba Olusegun Obasanjo Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sule Lamido ya ce akwai matasa a gwamnoni

Sule ya soki yadda matasa suke kukan an danne su, suna yin kira ga manya a siyasa su ba su wuri domin su rike madafan iko a yau.

Tsohon ministan harkokin wajen ya kawo misali da gwamnoni irin na jihohin Kogi, Katsina da Sokoto masu kananan shekaru a ofis.

Ya kuma bada misali da Yahaya Bello, wanda ya mulki jihar Kogi a baya yana da kananan shekaru.

Yadda Babangida ya nemi jawo matasa a mulki

Dattijon ya tuno da abin da gwamnatin sojin Ibrahim Badamasi Babangida ta yi, aka haramta tsofaffin ‘yan siyasa rike mukamai a kasa.

Duk wanda ya yi mulki daga 1960 har zuwa 1983, Janar Ibrahim Babangida ya hana shi rike kujera domin ba matasa dama a yi da su.

Alhaji Sule ya ce korar tsofaffi daga harkar mulki kamar mutum ne ya kashe wa yaro mahaifi saboda ya gaje shi tunda shekarunsa sun ja.

Kara karanta wannan

2027: Alkawarin da Pantami ya yi wa kiristoci a Gombe da ya kai ziyara coci

A karshe dai ya ce wanda ya kashe maka mahaifi, shi ne zai zama tamkar ubanka tunda yaro bai yi karfin da zai iya rike gida ba.

Rigimar Sanata Shehu Sani da Nasir El-Rufai

Rahoto ya gabata cewa Sanata Shehu Sani ya jero tulin mutanen da Nasir El-Rufai ya kama, ya ce abin da tsohon gwamnan ya shuka ne yake girma.

Kwamred yana ganin abin da Nasir El-Rufa'i ya yi na zalunci shi ne yake girba. Sanatan ya ce babu hannun shugaban kasa da Gwamna Uba Sani a lamarin.

Shehu Sani ya fadi abin da ya jawo aka rufe El-Rufai ya kuma ce babu zancen kishin Arewa, illa iyaka Bola Tinubu ya samu matsala da tsohon gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng