Yadda ‘Yan Sanda Suka Shiga Suka Fita Aka Damko Shugaban Ma’aikatar Bogi a Wani Kauye
- Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta damko Adeniyi Adeyemi wanda sunansa yanzu ya shiga sako da lunguna
- Alkali ya bada umarnin a kamo wannan mutumi wanda ya kafa kuma yake jagorantar hukuma ta bogi a Abuja
- Adeniyi Adeyemi ya kashe wayoyinsa domin a gaza gane inda yake, sai ya samu wani wuri ya boye a jihar Osun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Dakarun ‘yan sandan Najeriya sun kama Adeniyi Adeyemi wanda yake karyar rike da shugabancin wata hukuma ta bogi.
A sakamakon umarnin da wata kotun tarayya a Abuja ta bada na cafke shi, jami’an ‘yan sanda sun yi ram da shi domin a maka shi a kotu.

Source: Facebook
'Yan sanda sun damko Adeniyi Adeyemi
Jaridar Punch ta kawo rahoton yadda Adeniyi Adeyemi ya shiga hannu. Ana tuhumarsa da laifin yin karya da kuma shirya makarkashiya.

Kara karanta wannan
Bayan umarnin kotu, an kama shugaban hukumar bogi da ake ta cece kuce a kanta a Najeriya
Hadimin kakakin ‘yan sandan Najeriya, Aminu Koji ya tabbatar wa manema labarai cewa sun yi nasarar cafke Mista Adeniyi Adeyemi.
Daga baya tashar talabijin na TVC ta saki bidiyon shi a Youtube lokacin da ya shiga hannun hukuma.
Yadda DSS suka yi ta neman Adeniyi Adeyemi
Kafin jami’an tsaro su iya kama shi a jihar Osun, ma’aikata daga hukumar DSS sun shafe sama da mako guda suna neman Adeniyi Adeyemi.
An ce shugaban hukumar bogi ya kashe wayoyinsa da kwanaki biyu, wannan ya sa jami’an tsaro irinsu DSS suka gagara gane inda yake.
A karshe sai dai hukumar DSS ta hakura da neman inda yake. Wannan ya sa wasu jami’an kar-ta-kwana na ‘yan sanda suka shiga lalube.
Kokarin 'yan sanda karkashin CSP Moses Lohor
Wasu dakaru a karkashin jagorancin CSP Moses Lohor aka tura Osun su kamo Adeniyi Adeyemi.
Kafin yanzu CSP Lobor ya jagoranci wata rundunar ‘yan sanda da ke yaki da masu garkuwa da mutane a Osun, don haka ya san jihar.
Jami’in ‘dan sandan ya kawo zaman lafiya a kewayen Ilesa, amma a sakamakon harbe Kwamred Iyanda Alowonle aka kama shi, aka je kotu.
Sufetan ‘yan sanda na lokacin ya sa aka kai shi gaban alkali saboda zargin harbe shugaban tashar motocin Osun a sanadiyyar karamar rigima.
Vanguard ta ce a ce a safiyar Talata dakarun IRT suka damko Adeyemi daga mabuyarsa a Ijesa. Daga nan aka kai shi Ibadan, sai aka wuce Abuja.
Kakakin ‘yan sandan Osun, Abiodun Ojelabi ya tabbatar da an kama wanda ake neman, amma bai yarda ya yi wa 'yan jarida wabu karin bayani ba.
Adeyemi ya ci bashin N400m ya samu kujerar PFIPC
An rahoto Shugaban hukumar bogi ta PFIPC, Adeniyi Adeyemi, ya ce ya karɓi aron Naira miliyan 400 ne domin biyan kuɗin da aka nada shi shugaba.
Adeyemi ya musanta jita-jitar cewa yana shirin tserewa daga Najeriya ko kuma sanin wani shiri na neman mafaka a Amurka ta hannun wsu kamfani.
A yanzu rundunar 'yan sanda na shirin gurfanar da shi a gaban kotu kan zargi da suka shafi amfani da takardun bogi da kafa hukumar ba bisa ƙa'ida ba.
Asali: Legit.ng
