Mutane 4 da Suka Yi wa Atiku Abubakar Abokan Takara a Tarihi daga 2007 zuwa yau

Mutane 4 da Suka Yi wa Atiku Abubakar Abokan Takara a Tarihi daga 2007 zuwa yau

Atiku Abubakar ya shafe shekaru sama da 30 yana da burin ganin ya mulki Najeriya, ‘dan siyasar ya fara nuna sha’awarsa ne tun a 1992.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A wasu lokutan Alhaji Atiku yakan yi dace a tsaida shi takara, akwai sa’ilin da ko tutar fitowa takara a babban zaben shugaban kasa bai samu ba.

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Rahoton nan ya yi kokarin tattaro ‘yan siyasar da suka taya Atiku Abubakar takara, suka zama masa abokan gami bayan ya samu tikiti.

Tun lokacin da ya fara fitowa takara, Atiku yana zabo kirista daga bangaren Kudu maso gabas ko Kudu maso kudu domin ya zama abokin gaminsa.

Legit Hausa ta yi duba da abubuwan da suka faru a zabukan 2007, 2019, 2023 da kuma 2027 da ‘dan siyasar ya zama ‘dan takara na ADC.

Kara karanta wannan

An ba Tinubu shawarar wanda zai ɗauko a matsayin mataimakinsa a zaben 2027

Atiku
Alhaji Atiku Abubakar lokacin yakin neman zabe Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Abokan gamin Atiku Abubakar a takarar shugaban kasa

1. Ben Obi

A shekarar 2007 wanda shi ne karon farko da Atiku Abubakar ya samu tikitin tsaya wa takarar shugaban kasa, ya dauko Sanata Ben Obi ne.

Atiku ya zakulo ‘dan siyasar wanda ya wakilci yankin Anambra a Majalisar dattawa, ya nemi ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Daukar Obi ba ta kai ga shi nasara ba, AC ta zo bayan Umaru Yar'Adua (PDP) da Muhammadu Buhari (ANPP) a zaben da ake zargin an murde.

2. Peter Obi

Sai bayan shekaru 12 kuma aka sake tsaida Atiku a babban zabe, a nan ma kuma ya sake koma wa mutanen Kudu maso gabas su taya shi takara.

Har ila yau, daga Anambra tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya nemo abokin tafiyarsa, ya hada tikitinsa da Peter Obi mai farin jini a yankin.

Kara karanta wannan

Gwamnan Ekiti ya hadu da Tinubu, ya fadi adadin kuri’un da mutanesa za su ba APC

Tsohon gwamnan na Anambra ya taimaka wa tikitin PDP a 2019 kuma aka samu kuri’u miliyan 12 sai dai ba a iya doke Muhammadu Buhari ba.

3. Ifeanyi Okowa

A karawar da aka yi a 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya sake samun takara a PDP sai dai jam’iyyar hamayyar ta rasa manyan ‘ya ‘yanta gabanin zaben.

Ifeanyi Okowa lokacin yana gwamna a Delta shi ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP a lokacin, ya fito ne daga Kudu maso kudu.

Daukar Sanata Okowa bai yi wani tasiri ba domin tsohon mutuminsa, Peter Obi ya yi masa illa a yankin, hakan ya taimaka wajen nasarar Bola Tinubu.

Atiku
Alhaji Atiku Abubakar da abokan gaminsa a 2019 da 2027, Peter Obi da Rotimi Amaechi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

4. Rotimi Amaechi

Bayan jawo manyan ‘yan adawa zuwa ADC, babban ‘dan siyasar ya yi nasara a zaben tsaida gwani a kan Rotimi Amaechi da Mohammed Hayatu-Deeen.

Da jam’iyyar adawar ta ba shi tuta, Alhaji Atiku ya san yadda ya yi har ya lallabi tsohon gwamnan na Rivers ya lashe aman shi, ya zama abokin gaminsa.

Kara karanta wannan

Zargin badakalar N400m: Atiku ya bukaci Tinubu ya kori shugaban ma'aikatansa

Amaechi wanda ya yi minista a zamanin Muhammadu Buhari shi ne ‘dan takarar mataimakin shugaban kasar ADC, shi ma ya fito ne daga Neja Delta.

Tinubu zai doke Atiku, Obi a 2072?

Kwanaki da lashe zabensa, Gwamnan Ekiti ya fadi kuri’un da Bola Ahmed Tinubu zai samu a 2027, inda zai kara da ADC, PDP, NDC da sauran jam'iyyu.

Hasashen gwamna Biodun Oyebanji ya ba APC da Bola Tinubu ninkin baninkin na kuri’un 2023 domin kuwa wannan karo yana harin kuri'u akalla 600, 000 ne.

A lokacin da ya ziyarci fadar Aso Rock a Abuja, an rahoto gwamnan yana bayanin abubuwan da za su taimaka wa jam'iyyar APC a takarar da za a yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng