Akpabio Ya Kare Dangantakar Majalisa da Tinubu, Ya Fadi Dalili
- Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce Majalisar Dokoki za ta ci gaba da hada kai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Ya ce aikin 'yan majalisa shi ne kare muradun 'yan Najeriya, ba kirkirar rikici da bangaren zartarwa duk da adawar da wasu ke yi da hakan
- Yan adawa da wasu masu sharhi a Najeriya na zargin yan majalisa da zama 'yan amshin shatan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce Majalisar Dokoki ta Kasa za ta ci gaba da yin aiki tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu muddin hakan zai amfani Najeriya.
Akpabio ya bayyana hakan ne ranar Talata 14 ga watan Yuli, 2026 yayin bude taron makon majalisa na shekarar nan da aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan
'Yan sandan jihohi: Tinubu ya aika da bukatar gyara kundin tsarin mulki ga majalisa

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Akpabio ya jaddada cewa kundin tsarin mulki ya dora wa majalisa alhakin yi wa 'yan Najeriya hidima, ba tayar da rikici da bangaren zartarwa don nuna 'yancin kai ba.
Akpabio ya kare alaka da Tinubu
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Akpabio ya ce abin da ya dace shi ne majalisa ta goyi bayan duk abin da zai amfani kasa, ta yi tambayoyi kan abubuwan da ke bukatar bincike, sannan ta gyara inda ake bukatar gyara.
A cewarsa:
"Mun yi aiki tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin samun ci gaban kasa."
Ya kuma ce Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun yi aiki cikin fahimtar juna da girmama juna a cikin shekaru uku da suka gabata a kasar nan.
Bukatar Akpabio ga yan Najeriya
Sanata Godswill Akpabio ya ce majalisa ba ta 'yan majalisa ba ce, illa ta dukkannin 'yan Najeriya da kuri'unsu suka kafa ta a zaben da aka yi a kasar nan.

Source: Facebook
Ya ce:
"Ba za a saka shamaki tsakanin 'yan Najeriya da majalisa ba. An gina su ne domin maraba da su, ba a matsayin masu kallo kawai ba, har ma a matsayin masu dimokuradiyya na hakika."
Shugaban Majalisar Dattawan ya ce amincewar jama'a ga cibiyoyin dimokuradiyya tana kara karfi ne idan ana gudanar da aiki cikin gaskiya da rikon amana.
Ya bukaci 'yan Najeriya su halarci zaman sauraron ra'ayoyin jama'a, su karanta dokokin da majalisa ke yi, su rika yi wa 'yan majalisa tambayoyi tare da tuna masu nauyin da aka dora masu.
Tinubu zai ci zabe - Akpabio
A baya, mun wallafa cewa shugaban majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya ce kungiyar City Boy za ta taka rawa wajen tabbatar da sake zaben Shugaba Bola Tinubu a babban zaben 2027 mai zuwa.
Akpabio ya ce kungiyar za ta tabbatar shugaban kasa ya samu wakilai a dukkannin rumfunan zabe domin kare kuri'un da za a kada masa a mazabu da kananan hukumomin da ke a fadin Najeriya
Shugaban majalisar, wanda tsohon gwamna ne ya bukaci mambobin kungiyar su ci gaba da wayar da kan masu zabe tare da yin watsi da duk zarge-zargen da za su biyo bayan sakamakon zabe.
Asali: Legit.ng

