"Sauran Jam'iyyu Suna Bacci," Akpabio Ya Fadi yadda Tinubu Zai Lashe Zaben 2027

"Sauran Jam'iyyu Suna Bacci," Akpabio Ya Fadi yadda Tinubu Zai Lashe Zaben 2027

  • Shugaban majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya ce kungiyar City Boy za ta taka rawa wajen tabbatar da sake zaben Shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Akpabio ya ce kungiyar za ta tabbatar shugaban kasa ya samu wakilai a dukkan rumfunan zabe domin kare kuri'un da za a kada masa a fadin Najeriya
  • Ya bukaci mambobin kungiyar su ci gaba da wayar da kan masu zabe tare da yin watsi da duk zarge-zargen da za su biyo bayan sakamakon zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa kungiyar City Boy Movement na da karfin da zai taimaka wajen tabbatar da sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaben shekarar 2027.

Akpabio ya bayyana haka ne ranar Laraba yayin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar a ofishinsa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Yanzun nan rigima ta barke a majalisar wakilai kan bukatar a gayyaci Tinubu

Ya yabawa mambobin kungiyar bisa jajircewarsu da kuma abin da ya kira kishin kasa wajen gudanar da gangamin neman goyon baya ga Shugaba Tinubu domin ya sake samun wa'adi na biyu, in ji rahoton Vanguard.

A cewarsa, tasirin kungiyar ya fara bayyana a fadin Najeriya duk da cewa ba kowa ne ke iya ganinsa ba.

Ya ce City Boy Movement ta zama wata gagarumar kungiyar da jam'iyyun siyasa ke fara jin tasirinta kafin zaben 2027.

Akpabio ya kara da cewa daya daga cikin manyan ayyukan kungiyar shi ne tabbatar da cewa shugaban kasa yana da wakilai a dukkan rumfunan zabe a fadin kasar.

Ya ce da ace kungiyar ta kasance kafin zaben 2023, da kuri'u da dama da ba a kirga ba a wasu rumfunan zabe sun samu kariya.

Shugaban Majalisar Dattawan ya bukaci mambobin kungiyar su ci gaba da zagayawa sassan kasar domin wayar da kan masu zabe da kuma karfafa musu gwiwar shiga harkokin siyasa.

Ya kuma yi zargin cewa wasu jam'iyyun siyasa ba sa gudanar da irin wannan shiri, yana mai cewa hakan zai ba kungiyar damar samun nasara.

Akpabio ya ce idan aka sanar da nasarar Shugaba Tinubu a zaben 2027, akwai yiwuwar wasu su yi zargin an tafka magudi, amma ya bukaci mambobin kungiyar su yi watsi da irin wadannan maganganu.

Kara karanta wannan

'Abin da Tinubu ya kamata ya yi wa Gbajabiamila kafin binciken ICPC': Hadimin Atiku

Ya ce kamata ya yi matasa su yi amfani da wannan dama wajen koyon dabarun yakin neman zabe da jagoranci domin su zama shugabannin gobe.

Akpabio ya kara da cewa Majalisar Dattawa na goyon bayan matasan da suka zabi bin tafarkin da ya dace, yana mai jaddada muhimmancin gina matasa tare da ci gaba da mutunta dattawa saboda irin gogewar da suke da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com