Kalaman Sanata Graham na Karshe Sun Bayyana kafin Mutuwarsa a Amurka

Kalaman Sanata Graham na Karshe Sun Bayyana kafin Mutuwarsa a Amurka

  • Sanata Tommy Tuberville ya yi magana game da kalaman marigayi Lindsey Graham ya yi kafin mutuwarsa a kasar Amurka
  • A n ce Graham bai kira lambar gaggawa ta 911 ba, sai ma'aikaciyarsa ta yi hakan, inda jami'an ceto suka same shi cikin mawuyacin hali
  • Rahotanni sun ce Graham ya jinkirta neman kulawar likita saboda yana son kammala wasu muhimman ayyukan siyasa da suka shafi Rasha, Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Sanata Tommy Tuberville ya bayyana wasu bayanai kan kiran waya na ƙarshe da marigayi Sanata Lindsey Graham ya yi.

An samu bayanan ne jim kadan kafin rasuwarsa bayan dawowarsa daga wata tafiya da ya yi daga ƙasashen waje wanda ita ce tafiyarsa ta karshe.

Kalaman Graham na karshe kafin mutuwarsa
Sanata Lindsey Graham yana jawabi kafin rasuwarsa. Hoto: Tom Williams.
Source: Getty Images

Ciwon da ake hasashen ya kashe Graham

Kara karanta wannan

Adeyemi: 'Yadda na samo aron N400m wajen kafa hukumar bogi

A cewarsa, Graham ya kira mai tsara masa jadawalin aiki yana cewa yana fama da ciwon kirji kuma yana buƙatar a taimaka masa cikin gaggawa, cewar Fox News.

Tuberville ya ce ma'aikaciyar ta tambaye shi ko ya kira lambar gaggawa ta 911, amma Graham ya amsa cewa bai kira ba, shi ya sa ya kira ta.

Nan take ma'aikaciyar ta kira jami'an gaggawa na 911, a lokacin da ta isa gidan, jami'an sun riga sun karya ƙofa suna ƙoƙarin ceto rayuwarsa amma sai dai rai ya yi halin kafin nan.

Tuberville ya bayyana cewa marigayi Graham ya sadaukar da rayuwarsa wajen aiki, yana mai cewa kusan bai taɓa hutawa ba saboda yawan tafiye-tafiye da ayyukan siyasa.

Ya ƙara da cewa Graham kullum yana ƙoƙarin nemo hanyoyin warware matsalolin da suka shafi ƙasar Amurka da manufofinta na ƙasashen waje.

Rahoton Axios ya kuma bayyana cewa Graham ya jinkirta neman kulawar likita kafin wata hira da aka shirya yi da shi a Amurka lamarin da ya ba da mamaki.

Sanata Graham ya riga mu gidan gaskiya
Sanatan Amurka, Lindsey graham da Shugaba Donald Trump. Hoto: Donald J Trump, Lindsey graham.
Source: Facebook

Alfaharin da marigayi Graham ya yi

Rahoton ya ce Graham ya bayyana cewa ba zai iya mutuwa a lokacin ba domin har yanzu yana son kammala batun takunkumin Rasha da kuma warware matsalolin Iran, cewar CNN.

Kara karanta wannan

Umahi: Ma'aikaciyar jinya ta mutu a gida Minustan Tinubu, an zarge shi da boye gaskiya

An kuma ruwaito cewa yana son ci gaba da ƙoƙarin daidaita dangantaka tsakanin Isra'ila da Saudiyya kafin rasuwarsa sai dai Allah bai ba shi damar kammala shirin da ya yi niyya ba.

Waɗannan bayanai sun fito ne daga hirar da Sanata Tommy Tuberville ya yi, tare da rahoton Axios da ya bayyana abubuwan da suka faru a sa'o'in ƙarshe na rayuwar Lindsey Graham.

Abin da Graham ya yi ga Iran

Mun ba ku labarin cewa Sanata Lindsey Graham ya yi martani cikin rashin tsoro ga barazanar Iran kwanaki biyar kafin rasuwarsa a Amurka.

Graham ya rasu yana da shekara 71 sakamakon gajeriyar rashin lafiya, bayan ya dawo daga ziyarar Ukraine lamarin da ya tayar da kura a Amurka.

Rasuwarsa ta girgiza Amurka da ƙasashen duniya, yayin da Shugaba Donald Trump da sauran jagorori suka bayyana alhininsu inda suka bayyana sanatan a matsayin jarumi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.