'A Zagi Kwankwaso Kai Tsaye:' NDC Ta Mayar wa Sanata Hanga Martani kan Takarar Kano

'A Zagi Kwankwaso Kai Tsaye:' NDC Ta Mayar wa Sanata Hanga Martani kan Takarar Kano

  • Shugaban jam'iyyar NDC na shiyyar Arewa, Muhammad Rabi'u Bakin Zuwa, ya mayar da martani ga kalaman Sanata Rufa'i Sani Hanga
  • Ya ce ba su taba gaya wa Sanata Hanga cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne ya aike su gidansa ba a lokacin da aka yi zancen takarar Mustapha Kwankwaso
  • Wannan martani na zuwa ne bayan wadansu zarge-zarge da Sanata Rufa'i Hanga ya yi game da takarar gwamna da na mataimakin gwamnan Kano a NDC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Shugaban jam'iyyar NDC na shiyyar Arewa, Muhammad Rabi'u Bakin Zuwa, ya yi martani ga kalaman Sanata Rufa'i Sani Hanga, mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.

Sanata Hanga, wanda jigo ne a tafiyar Kwankwasiyya, ya yi wasu kalamai masu kama da sukar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da kuma yadda aka zaɓi ɗan takarar gwamna a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kwankwason APC ya ari bakin 'yan Arewa, ya yi magana kan tikitin Tinubu da Shettima a 2027

NDC ta soki kalaman Hanga
Sanata Rufa'i Sani Hanga tare da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @SaifullahiHon
Source: Facebook

A martanin da ya yi cikin wata hira da Siyasarmu TV, wadda aka wallafa a shafin Facebook, Muhammad Rabi'u Bakin Zuwa ya ce tabbas sun ziyarci gidan Sanata Hanga.

Abin da aka tattauna da Rufai Hanga

Muhammad Rabi'u Bakin Zuwa ya bayyana cewa shi tare da shugaban jam'iyyar NDC na jihar Kano sun je gidan Sanata Hanga, amma ba su shaida masa cewa Kwankwaso ne ya aike su ba.

A kalamansa:

"Lokacin da muka tafi, ni da Mai Riga muka je gidansa. Wallahil Azeem, ba mu ce masa Kwankwaso ne ya turo mu ba. Mun ce masa ga wata ajanda da muka zo da ita, wadda muke so shi ma ya ba da goyon baya domin ta tabbata."

Ya ci gaba da cewa:

"Ya ce wannan abu ya masa daidai. Wallahi, Tallahi, yadda yake ganin yaron nan da mutunci, ko shi ne ma yake kan kujera aka ce ya sauka ya bai wa Mustapha, zai sauka ya bar wa Mustapha."

Kara karanta wannan

Kano APC: 'Ayyukan da za su jawo wa Tinubu ruwan kuri'a a 2027'

Kwankwaso mutum ne kamar kowa - NDC

Jagoran jam'iyyar NDC ya bayyana cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso mutum ne kamar kowa, saboda haka bai ga dalilin da zai sa a ce ba ya ɗaukar shawara ba.

Bakin Zuwa ya ƙara da cewa an ba Kwankwaso shawara, har ma an matsa masa lamba, kuma ya amince NDC ta tsayar da ɗansa a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna a jihar Kano.

NDC ta ce dole aka yi wa Kwankwaso don tsayar da dansa takara
'Dan takarar mataimakin gwamna a NDC Mustapha Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Ya kuma ce duk wanda ke son ya zagi Kwankwaso ya yi hakan kai tsaye, ba tare da fakewa da cewa jagoran ba ya karɓar shawara ko umarni ba.

Waɗannan kalamai sun biyo bayan zargin da Sanata Rufa'i Sani Hanga ya yi cewa Kwankwaso ya turo tawaga zuwa gidansa domin sanar da shi shirin tsayar da Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano.

Sai dai Hanga ya ce daga baya bai san yadda aka yi ba sai aka ji an tsayar da tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, a matsayin ɗan takarar gwamna.

Kara karanta wannan

Martanin El Rufa'i ga ICPC kan zargin ganawar siyasa a asibiti

Yaron Kwankwaso ya samu takara a NDC

A baya, mun wallafa cewa jam'iyyar NDC da dan takararta na gwamna a jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, sun sanar da wanda zai yi takarar mataimakin gwamna a babban zaben 2027 da ke tafe.

An bayyana Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin abokin takarar Aminu Abdulsalam Gwarzo a zaben 2027 da ake tunkara wanda za su hadu wajen fafatawa da gwamna Abba Kabir Yusuf da Murtala Sule Garo.

Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso ya kasance haifaffen da ne ga madugun Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Kano sannan ya rike mukamin kwamishina kafin su raba gari da gwamnatin Abba Kabir Yusuf da ta koma APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng