Zamfara: An Kakaba Haraji ga Jama'a bayan Nada Sabon Kwamandan 'Yan Bindiga

Zamfara: An Kakaba Haraji ga Jama'a bayan Nada Sabon Kwamandan 'Yan Bindiga

  • Rahotanni sun ce ’yan bindigar Ado Aleiro sun nada sabon kwamanda bayan kashe Kachalla Iliya Mai Rasha
  • Ana zargin wakilan ’yan bindigar sun kakaba harajin N200,000 ga kowane kauye a yankin karamar hukumar Tsafe
  • Hatsabiban 'yan bindigan na shirin tara kusan N25m domin sabon kwamandan ya sayi makamai da alburusai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Wasu majiyoyin leken asiri sun ce ’yan bindigar da ke karkashin fitaccen jagora, Ado Aleiro, sun nada sabon kwamandan da zai jagoranci ayyukansu bayan kashe Kachalla Iliya Mai Rasha.

Rahotanni sun nuna cewa kungiyar na kokarin sake tsara ayyukanta a jihar Zamfara bayan mutuwar Mai Rasha.

'Yan bindiga sun kakaba haraji a Gombe
Taswirar jihar Gombe, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Majiyoyi sun bayyana cewa har yanzu ba a bayyana sunan sabon kwamandan ba. Sai dai ana zargin wakilan ’yan bindigar sun kakaba harajin N200,000 ga kowane kauye da ke yankin yammacin karamar hukumar Tsafe.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun nuna rashin imani kan mata da jarirai a wani kazamin hari a Katsina

An kakaba haraji a kauyuka

A cewar majiyoyin, ana son tara kusan N25m daga harajin domin sabon kwamandan ya sayi karin makamai da alburusai.

Rahotanni sun kuma ce an binne akalla kwamandojin ’yan bindiga 10, wadanda ake kira Kachallai, a kauyen Kizara da ke yammacin Tsafe.

An ce an binne su ne bayan wasu hare-haren sojoji da aka gudanar a baya-bayan nan, yayin da wasu daga cikin ’yan bindigar suka samu raunuka daban-daban.

’Yan bindiga sun yi nisa neman dabbobi

Wasu mazauna yankin da suka saba da yadda kungiyoyin ’yan bindigar ke motsi sun ce masu komowa daga hare-hare suna sanar da abokan huldarsu cewa yanzu suna yin tafiya mai nisa zuwa yankuna masu nisa domin neman dabbobi.

A cewarsu, ’yan bindigar suna ikirarin cewa dabbobi sun yi karanci a jihar Zamfara sakamakon ci gaba da ayyukan tsaro da kuma yawan satar shanu.

Sai dai ba a samu damar tabbatar da wadannan rahotanni daga wasu majiyoyi masu zaman kansu ba.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi da 'yan bindiga suka nemi N80m bayan sace basarake

Majiyoyin tsaro sun ce suna sa ido kan rahoton nada sabon kwamandan da kuma zargin karbar haraji daga al’ummomin karkara.

An ce ana gudanar da wannan bincike ne a matsayin wani bangare na kokarin tattara bayanan sirri domin gano hanyoyin samar da kayan aiki da samun kudin kungiyoyin ’yan bindigar.

'Yan bindiga sun kakaba haraji a Zamfara
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Sojoji sun kara matsa lamba

Ayyukan sojoji karkashin Operation Fansan Yamma sun kara matsa lamba kan maboyar ’yan bindiga a jihohin Zamfara, Katsina da Sokoto a makonnin baya-bayan nan.

Rahotanni sun ce ayyukan sun yi sanadin kashe wasu fitattun kwamandojin ’yan bindiga tare da tarwatsa wasu daga cikin sansanoninsu.

'Yan bindiga sun kashe sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga dauke da manyan makamai sun kashe aƙalla sojoji shida tare da yin garkuwa da fiye da mutum 70 a jihar Zamfara.

'Yan bindigan sun kai harin ne a garin Kasuwar Daji da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng