Adeniyi: 'Yadda Na Samo Aron N400m wajen Kafa Hukumar Bogi'

Adeniyi: 'Yadda Na Samo Aron N400m wajen Kafa Hukumar Bogi'

  • Shugaban hukumar bogi ta PFIPC a Najeriya, Adeniyi Adeyemi ya kawo karshen zarge-zarge a kan yadda ya samu kudin gudanar da hukumar
  • Sunan Adeniyi ya karade Najeriya da kasashen waje bayan an gano yan nada kansa shugaban wata hukuma da ake zargin ya kirkira da takardun bogi
  • Da farko an yi zargin akwai hannun shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila a cikin kafa hukumar amma Adeniyi ya yi karin bayani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban hukumar PFIPC da gwamnati ta ce na bogi ne, Adeniyi Adeyemi, ya bayyana halin da ake ciki game da yadda ya samu kudin gudanarwa.

Ya bayyana cewa ya karɓi bashin Naira miliyan 400 domin samun takardar naɗinsa, kuma mutanen da suka ba shi kuɗin sun kai ƙorafi ga Hukumar EFCC suna neman a mayar masu da kuɗinsu.

Kara karanta wannan

PFIPC: Shugaban hukumar bogi ya soki binciken ICPC, ya aika sako ga Shugaba Tinubu

Adeyemi ya ce N400 aka ba shi aro don kafa hukumar PFIPC
Shugaban hukumar bogi ta PFIP Adeniyi Adeyemi a ofis Hoto: Adeniyi Adeyemi
Source: Facebook

Adeyemi ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Litinin, 13 ga watan Yuli, 2026 a lokacin da gwamnati ke ci gaba da shari'a da shi.

Zargin da Adeyemi ya yi

Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa wannan karin bayani na Adeyemi na zuwa ne makonni kaɗan bayan ya zargi shugaban ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, da karɓar kuɗin ta hannun wani domin a ba shi mukamin.

Ya ce:

"Na karɓi bashin wannan kuɗi. Waɗanda suka ba ni bashin sun kai ƙorafi ga EFCC suna neman in dawo musu da kuɗinsu. Na karɓi bashin ne domin biyan kuɗin wannan naɗi.a

Adeniyi Adeyemi ya kuma zargi gwamnatin tarayya da yi masa rashin adalci, yana mai cewaan saka shi a cikin wani hali tare da kunyata shi a idon duniya.

Adeyemi ya magantu kan neman mafaka

Da aka tambaye shi rahotannin da ke cewa wani kamfanin lobi na Amurka yana taimaka masa wajen neman mafaka, Adeyemi ya ce bai san da wannan shiri ba, sai dai ya karanta labarin ne kamar kowa.

Kara karanta wannan

2027: Fadar shugaban kasa ta yi magana kan barazanar kashe Peter Obi

Ya ƙara da cewa an dakatar da shafukansa na kafafen sada zumunta, lamarin da ya sa ba ya samun cikakken bayani kan abin da ke faruwa.

Adeyemi ya ce an kai shi EFCC
Prince Adeniyi Adeyemi Matthew ya buga tagumi Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Adeyemi ya kuma musanta jita-jitar cewa yana shirin tserewa daga Najeriya, inda ya bayyana cewa yana gida bai je ko'ina ba tukunna.

A kalamansa:

"Har yanzu ina Najeriya. Ba zan je ko'ina ba."

A ranar 11 ga Yuni, Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar da sanarwar cewa babu wata hukuma mai suna PFIPC a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, tare da bayyana Adeyemi a matsayin mai gabatar da kansa a matsayin jami'in gwamnati ba bisa ka'ida ba.

Gwamnati ta fara shari'a da Adeyemi

A baya mun wallafa cewa rundunar 'yan sandan Najeriya za ta gurfanar da Adeniyi Adeyemi a gaban kotu kan zarge-zargen da suka shafi kafa hukumar PFIPC ba baisa ka'ida ba da amfani da takardun bogi.

Ana zargin Adeniyi Adeyemi da jagorantar wata hukuma mai suna PFIPC wadda gwamnati ta ce ba ta san da zamanta ba duk da yadda hukumar ta rika gudanar da ayyukanta da wasu daga cikin jami'an gwamnati.

Manyan jami'an gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da wasu mutane ake sa ran za su ba da shaida a shari'ar, inda ake tuhumar kansa da samar da takardar bogi da ta nada shi a matsayin shugaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng