Takarar Abba Ta Kara Samun Karfi Kwanaki da Samun Goyon Bayan Izala da Darika

Takarar Abba Ta Kara Samun Karfi Kwanaki da Samun Goyon Bayan Izala da Darika

  • Kwamishinan labarai ya karɓi bakuncin tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi da aka yi a Kano a 1997/98
  • Tsohon shugabannin ƙananan hukumomi da kansilolin sun ziyarce shi, suna nuna goyon baya ga gwamnatinsu
  • Kafin ya kai rokonsu wajen Gwamna abba kabir yusuf, Ibrahim Waiya ya bai wa tsofaffin ‘yan siyasar N3m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Ibrahim A. Waiya ya yi zama da wasu tsofaffin ‘yan siyasa da suka rike shugabanci a kananan hukumomin jihar Kano a baya.

Kwamishinan yada labaran ya bayyana cewa an yi zaman ne da nufin nuna goyon baya ga Abba Kabir Yusuf da yake neman tazarce a 2027.

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da wani taron jam'iyyar APC a Najeriya Hoto: Kano a construction site
Source: Facebook

Kwamishina ya hadu da tsofaffin ciyamomi & kansiloli

Kwamred Ibrahim A. Waiya a shafin X da aka fi sani da Twitter ya bayyana zaman da ya yi da tsofaffin shugabannin kananan hukumomin Kano.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bangar siyasa suka hallaka wani fitaccen malamin Islamiyya a Bauchi

Tsofaffin shugabannin kananan hukumomi da kansilolin sun yi mulki ne a 1997 da 1998 kafin sojoji su mika mulki ga 'yan farar hula a Najeriya.

Ya ce waɗannan jagororin siyasa ne masu daraja, waɗanda ba za a manta gudunmawarsu wajen gina dimokraɗiyya da nasarorin zaɓe ba.

Sun tabbatar wa Kwamishinan cewa za su ci gaba da wayar da kan jama'a da kuma tallafa wa manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

“A yau, na karɓi bakuncin ziyarar ban girma daga kungiyar tsofaffin Shugabannin Ƙananan Hukumomi da Kansiloli waɗanda suka yi aiki a lokacin 1997/1998.
“Sun zo ne domin gaishe shi da nuna goyon baya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta hannun ofishina.

Tsofaffin 'yan siyasan sun roki Abba hakkokinsu

Bugu da ƙari, ƙungiyar ta yi roƙo ga Abba Kabir ya duba batun hakkokinsu na ritaya, kamar yadda gwamnatin Kano ta yi wa takwarorinsu a baya.

Kwamishinan ya nuna godiya sosai da suka zaɓi ziyartar ofishinsa, kuma ya yi masu alkawarin zai ci gaba da taimaka musu yadda ya kamata.

A matsayin somin-tabi, kwamishinan harkokin yada labaran ya cire N3m daga aljihunsa ya ba kungiyar kamar yadda ya shaida a dandalin X.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya shiga lamarin tsare El Rufai da barazanar kashe Peter Obi

Game da ragowar bukatun nasu, Ibrahim Waiya ya yi alkawarin zai mika rokonsu ga Mai girma gwamna wanda suke mara masa baya a APC.

Waiya ya bayyana cewa yana mai alfahari da wannan ziyara a madadin mai gidansa, Abba Kabir Yusuf.

Har ila yau, ya yi alkawarin zai cigaba da taimaka masu a duk lokacin da ya samu dama, yana mai fatan su yi aiki tare da nufin cigaban Kano.

Kungiyar Izala za ta zabi Abba a 2027

Labari ya zo cewa reshen kungiyar Izala (JIBWIS) na Jihar Kano ya bayyana goyon bayansa ga Abba Kabir Yusuf domin tazarce a zaben gwamna.

Shugaban kungiyar na jihar, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya bayyana cewa ayyukan raya kasa da gwamnatin ke yi sun cancanci a ci gaba da su.

Farfesa Abdullahi Saleh ya fadi haka ne lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarce shi a gidansa domin yi masa ta'aziyyar rasuwar matarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng