Sakon Gwamnan Kano, Abba Gida Gida ga Lauyoyi game da Zaben 2027

Sakon Gwamnan Kano, Abba Gida Gida ga Lauyoyi game da Zaben 2027

  • Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya zaburar da lauyoyi game tabbatar da nasarar babban zaben 2027 da ke tunkaro Najeriya
  • Gwamnan, da ake yi wa lakabi da Abba Gida Gida ya bayyana cewa lauyoyi suna da matukar muhimmanci wajen tabbatar da dimokuradiyya
  • Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kuma yi karin bayani game da matasan lauyoyi sama da 70 da ya dauka aiki tare da aiwatar da inganta iliminsu a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci lauyoyi da su tsaya tsayin daka wajen kare doka tare da taimakawa wajen tabbatar da an gudanar da zaben shekarar 2027 cikin lumana, adalci da gaskiya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Alhamis 9 ga watan Yuni, 2026.

Kara karanta wannan

Ministan Tsaro: Abin da ya hana sojoji gwabza wa da ƴan bindiga don ceto ɗaliban Oyo

Gwamnan Kano ya shawarci lauyoyi a kan tabbatar da gaskiya a sha'anin zabuka
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto; Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

A cikin sakon da Sanusi Bature ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake kaddamar da taron shekara na biyu na Arewa Young Lawyers' Forum, wanda aka gudanar a dakin taro na Amani Event Centre da ke Kano.

Abba ya fadi muhimmancin lauyoyi

Sanarwar ta kara da cewa Abba Gida Gida ya ce lauyoyi na taka muhimmiyar rawa wajen kare martabar tsarin shari'a, musamman a lokutan shari'o'in da suka shafi zabe kafin da bayan gudanar da zabe, domin tabbatar da adalci.

A cewarsa, matasa lauyoyi su ne ginshikin dorewar dimokuradiyya, kare hakkin 'yan kasa da tabbatar da bin doka, yana mai cewa su ne kan gaba wajen sanin kalubalen sana'arsu a yau.

Gwamnan ya kuma bayyana irin goyon bayan da gwamnatinsa ke bai wa bangaren shari'a. Ya ce gwamnatin Kano ta dauki matasa lauyoyi sama da 70 aiki tare da rabawa sama da 100 kwamfutocin tafi-da-gidanka.

Kara karanta wannan

Bayan Darika, Izala ta fadi dan takarar gwamnan da za ta zaba a Kano a 2027

Gwamnatin Abba na inganta aikin lauyoyi a Kano

Ya kara da cewa gwamnatin ta tabbatar da biyan alawus-alawus na kayan ofis da rigunan aiki a kan lokaci, tare da aiwatar da shirye-shiryen horaswa da kara wa jami'an da ke aiki a bangaren shari'a.

Haka kuma, ya ce gwamnati ta inganta tsarin gudanar da shari'a ta hanyar sauye-sauyen hukumomi da kuma karfafa amfani da hanyoyin sasanci wajen warware rikice-rikice.

Gwamnan Kano ya ce lauyoyi suna da amfani wajen tabbatar da dimokuradiyya
Gwamna Abba Kabir Yusuf yana jawabi a wani taro a jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa shugabannin Arewa Young Lawyers' Forum karkashin jagorancin Umar A. Chiroma saboda shirya taron.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa zai samar da tattaunawa mai amfani da kuma taimakawa wajen bunkasa sana'ar lauya a Arewacin Najeriya.

Gwamnatin Abba ta juyo kan samar da ruwa

A baya kun samu labarin cewa gwamnatin jihar Kano ta sake share hawayen wasu daga cikin mazauna karkara da ke fama da rashin ruwan famfo saboda lalacewa matatar ruwa da aka shafe shekaru ana fama da ita.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya nuna damuwa kan gargadin da Majalisar ɗinkin duniya ta yi wa Arewacin Najeriya

Kwamishinan Albarkatun Ruwa Dr. Dahir M. Hashim ya sanar da cewa al'ummomi za su fara karbar ruwa tun ranar Talata ta 8 ga Yuli 2026 bayan gyaran da ake yi, inda tun a lokacin ta fara fitar da ruwa mai kyau.

Kwamishinan ya sanar da cewa an sanya sabon injin lantarki na 800 kVA kuma an gyara injunan fitar ruwa a matsayin wani bangare na gyaran tsarin, sannan gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da gyara matatun da ake da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng