Martanin El Rufa'i ga ICPC kan Zargin Ya Yi Ganawar Siyasa a Asibiti
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi martani ga zargin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC
- Hukumar ta yi zargin cewa El-Rufa'i ya karya ka'idojin da aka gindaya masa, musamman a lokacin da aka sahale masa ya ga likita a asibiti
- Mai taimaka wa tsohon gwamnan jihar Kaduna kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya yi karin bayani a kan canjin da ICPC ta yi wa El-Rufa'i
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Mai taimaka wa tsohon gwamnan jihar Kaduna kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya ce Nasir El-Rufai bai take umarnin kotu ba yayin da ya je asibitin Abuja domin a duba lafiyarsa.
Adekeye ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 9 ga watan Yuli, 2026 inda ya ce ikirarin da hukumar ICPC ta yi ba gaskiya ba ne.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta zagi El-Rufa'i da tattaunar siyasa a ziyarar ganin likita zuwa taron siyasa.
Hadimin El-Rufa'i ya wanke mai gidansa
Jaridar The Cable ta kawo labarin cewa a ranar Talata 7 ga watan Yuli, 2026 ne ICPC ta kama Farfesa Bello Abubakar, likitan El-Rufai, bisa zargin bayar da bayanan karya bayan ya duba tsohon gwamnan.
Mai magana da yawun ICPC, Okor Odey, ya ce El-Rufai da likitansa sun yi amfani da damar da aka ba su ta hanyar da ba ta dace ba, tare da karya umarnin kotu da ya shafi ziyarar duba lafiyarsa.
Sai dai Adekeye ya ce bayan El-Rufai ya gama ganawa da likitansa, Farfesa Bello Abubakar, wanda ƙwararren likitan cutar daji ne, ya zauna a kan rahoton likita da ICPC ta bukata kafin a mayar da shi inda ake tsare da shi.
Mutanen da El-Rufa'i ya gana da su
Ya ce wasu mutane da suka ji cewa zai je asibitin sun nemi ganin El-Rufa'i, daga ciki har da Isa Ashiru, yayin da wasu kuma suka gaishe shi ne kawai bayan sun hango shi.
Adekeye ya ce:
"Ikirarin ICPC cewa an mayar da ziyarar likita zuwa taron siyasa bai yi daidai da abin da ya faru ba."

Source: Facebook
Ya kara da cewa ICPC ce ta zabi lokacin ziyarar, ta kula da duk wanda ya shiga wajen, sannan jami'anta suna wurin tsawon lokacin. Har ila yau, ya ce ICPC ba ta bayyana takamaiman umarnin kotun da El-Rufai ya karya ba da har aka kai ga kama likitansa.
A cewarsa, umarnin da Mai Shari'a Aikawa ya bayar ranar 1 ga Afrilu, 2026 ya ba El-Rufai damar samun kulawar likita yayin da yake tsare, amma bai hana ko kayyade mutanen da za su iya ganinsa ba.
Atiku ya ja kunne kan El-Rufa'i
A baya, mun wallafa cewa 'dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC tiku Abubakar ya gargadi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu game da jagororin adawa, Peter Obi da Nasir El-Rufa'i.
Ya bayyana haka ne a yayin da 'dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi ya yi ikirarin ana neman rayuwarsa, kuma ba lallai ya kai babban zaben 2027 ba saboda barazanar da ya ke ciki.
Shi ma Nasir El-Rufa'i na garkame a hannun hukumar ICPC yayin da iyalansa ke kukan an haramta masa ganin likita tare da kama wanda ke kula da lafiyarsa, lamarin da Atiku ya ce abin takaici ne.
Asali: Legit.ng


