Abin da Saudiyya Ta Fada wa Trump Wanda Ya Jawo Fasa Kai Hari a Ƙasar Iran

Abin da Saudiyya Ta Fada wa Trump Wanda Ya Jawo Fasa Kai Hari a Ƙasar Iran

  • Shugaba Donald Trump ya ce ƙawayensu a Gabas ta Tsakiya sun cimma muhimman sharuɗɗan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin Iran
  • Ya bayyana cewa yarjejeniyar za ta haɗa da buɗe mashigin Hormuz gaba ɗaya, tare da dakile barazanar shirin nukiliyar Iran idan an cimma matsaya
  • Isra'ila ta amince da haɗa kai da Amurka wajen kammala yarjejeniya, amma Iran ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan ikirarin Trump ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a daren Asabar cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙi da Iran.

Ya ce ƙawayensu a Gabas ta Tsakiya sun cimma muhimman sharuɗɗan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin Iran da ake yi tsawon watanni biyar.

Saudiyya ta shawarci Trump kan ci gaba da yaki da Iran
Shugaban Amurka, Donald Trump tare da Yariman Saudiyya, Muhammad bin Salman, suna tattaunawa a Washington, DC. Hoto: Chip Somodevilla.
Source: Getty Images

Trump ya dakatar da farmaki a Iran

Kara karanta wannan

An cimma matsaya da Hamas, Trump zai fatattaki Isra'ila a Gaza

Trump ya ce saboda wannan ci gaba, ya amince da dakatar da shirin kai sabbin hare-hare kan Iran domin bai wa tattaunawar zaman lafiya damar samun nasara, cewar AP News.

Ya ƙara da cewa yarjejeniyar da ake shiryawa za ta haɗa da buɗe mashigin Hormuz gaba ɗaya, tare da kawo ƙarshen barazanar shirin nukiliyar Iran.

A cewarsa, matakin zai amfani duniya baki ɗaya, tare da ba Iran damar samun zaman lafiya da ci gaba idan aka cimma cikakkiyar yarjejeniya cikin gaggawa.

Trump ya kuma bayyana cewa Isra'ila ta amince ta yi aiki tare da Amurka domin kammala yarjejeniyar da za ta kawo ƙarshen yaƙin da ake yi.

Sai dai har zuwa lokacin wallafa rahoton, Iran ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance domin mayar da martani kan sabon ikirarin da shugaban Amurka ya yi.

Sanarwar Trump ta zo kwana guda bayan ya nuna cewa yana dab da sake ba da umarnin kai manyan hare-hare domin tilasta Iran komawa teburin tattaunawa.

Musabbabin dakatar da kai hari Iran bayan shawarar Saudiyya
Shugaban Amurka, Donald Trump jim kadan bayan jawabi ga 'yan majalisar Republican a Doral, Florida. Hoto: Roberto Schmidt.
Source: Getty Images

Abin da Saudiyya ta tattauna da Amurka

Rahotanni sun ce Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman ya tattauna da Trump ta waya, inda ya nuna damuwa kan yiwuwar ƙara tsananta yaƙin kafin wannan sanarwa.

Kara karanta wannan

Minista ya cire tsoro, ya fadi babban abin da ke rura wutar ta'addanci a Najeriya

Rahoto ya ce tattaunawar ta gudana ne a daidai lokacin da Trump ke nazarin ko zai ba da umarnin kai sabbin hare-hare kan Iran, cewar The Guardian.

An ce Saudiyya na fargabar cewa idan Amurka ta kai hari kan cibiyoyin makamashin Iran ko kuma ta lalata manyan gadoji da tashoshin wutar lantarki, Iran na iya mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan cibiyoyin makamashi na Saudiyya da sauran ƙasashen yankin Tekun Fasha.

A yayin kiran na ranar Asabar, Yarima Mohammed bin Salman ya nemi Trump ya fayyace irin sabon matakin da yake tunanin ɗauka kan Iran, kamar yadda mutumin ya bayyana.

Trump ya yi wa Iran barazana

An ji cewa Donald Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da kai wa Iran hare-hare masu tsanani a cikin makonni huɗu masu zuwa.

Ya yi ikirarin cewa hare-haren sun raunana karfin sojin Iran, yana mai cewa kasar ta rasa manyan rundunoninta.

Shugaba Trump ya kuma ce an samu fahimtar juna da Isra’ila kan shirin kwance damarar Hamas ta hanyar ajiye makamansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.