'Pantami Bai fi Sheikh Jingir ba': An Kalubalanci Yaran Farfesa da Ke Zagin Rarara
- Wani matashin malamin Musulunci, Isma'il Maiduguri, ya soki masu goyon bayan Farfesa Isa Ali Pantami kan yadda suka mayar da martani ga wakar Dauda Kahutu Rarara
- Isma'il ya ce magoya bayan Pantami sun yi shiru lokacin da Soja Boy ya zagi Sheikh Sani Yahaya Jingir, amma suka yi Allah-wadai da Rarara
- Malamin ya ce Rarara ya soki Pantami ne a matsayinsa na ɗan siyasa, yana mai zargin wasu da nuna son rai da fakewa da addini
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wani matashin malamin addinin Musulunci ya ja hankalin masu goyon bayan Farfesa Isa Ali Pantami a siyasance.
Isma'il Maiduguri ya ja kunnensu ne bayan fitar da sabuwar wakar da Dauda Kahutu Rarara ya yi da ake ta maganganu.

Source: Facebook
Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Lahadi.
Isma'il Maiduguri ya soki yaran Pantami
A cikin bidiyon, ya zargi magoya bayan Isa Ali Pantami da son rai yadda suka sukar Rarara saboda wakar da ya yi.
Sai dai ya ce akwai rashin adalci duba da yadda Soja Boy ya zagi Sheikh Sani Yahaya Jingir amma ba su ce komai ba.
Ya ce:
"Nan fa Soja Boy ya ci wa Sheikh Sani Yahaya Jingir mutunci ya yi masa zagin kare dangi, duk kika yi gum.
"Wannan ba malami ba ne, shi ya halatta a zabe shi ko saboda shi kun saba ra'ayin siyasa yana yin Muslim Muslim.
"Nan fa kuka halatta wa kanku zagin Jingir domin yana tallata Muslim Muslim, dattijo mai shekaru, yana da 'ya'ya mutum mai mutunci da runduna shiyasa na ce ba maganar kare addini ba ne da malamai siyasa ce kuma fake da ita bayan addini."

Source: Facebook
Malam ya fadawa yaran Pantami gaskiya
Isma'il Maiduguri ya ce idan gaskiya suke bi ya kamata su caccaki Soja Boy tun da shi ma ya zagi malamin addini da kuma cin mutunci mai tsanani.
Ya kara da cewa Rarara ya zagi malam ne a matsayinsa na dan siyasa amma ba wai malamin addini ba.
Har ila yau, Aramma Isma'il ya ce abin takaici ne yadda shi ma ake zafinsa saboda kawai bai fadan abin suke so ko wanda ya yi daidai da ra'ayinsu.
"Idan gaskiya ne meyasa ba ku yi wa Soja Boy tas kamar yadda kuke yi wa Rarara yanzu, Rarara ya soki malam ne a matsayin ɗan siyasa, lokacin da suke jam'iyya daya ya yi wa malam waka mai dadi muka fansu suna rungumar juna.
"Jingir bai yin takara al'ummarsa kawai yake fadawa ra'ayinsa amma kuka halatta wa kansu zaginsa, Soja Boy ya zage shi ba ku ce komai ba, ba ku yana zagin malamin addini ba.
"Nima kun halatta wa kanku ku zage ni, nima tsohon mai jan baki ne, aramma ne ni, baba na ma aramma ne, saboda ni bana fadan abin da ranku ke so."
- Isma'il Maiduguri
Pantami: Wakar Rarara ta jawo magana
An ji cewa fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara ya fitar da sabuwar wakar siyasa da ta shafi Farfesa Isa Ali Pantami, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a Arewa.
A cikin wakar, Rarara ya yi kalaman da suka fusata wasu, inda masu suka suka ce bai dace a ci mutuncin Pantami ba saboda matsayinsa.
Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya ce adawa da Pantami ya kamata ta kasance bisa hujjoji da bambancin siyasa, ba cin mutunci ba.
Asali: Legit.ng


