Abin da Pantami Ya Fada wa Sule Lamido a Taron ‘Yan Takaran PDP a Jigawa
- Isa Ali Ibrahim Pantami da wasu ‘yan takara da manyan magoya bayansa sun ziyarci Sule Lamido a gidansa a jihar Jigawa
- Malamin addinin da yanzu yake neman gwamnan Gombe ya kwarara yabo na musamman ga jagoran na jam’iyyar PDP
- Sheikh Pantami ya kira Sule da uba kuma jagora mai son talaka wanda ya tsotso wannan akida tun daga Malam Aminu Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Jigawa - Isa Ali Ibrahim Pantami ya ziyarci Sule Lamido yayin da yake kokarin ganin ya samu gwamna a jihar Gombe a karkashin PDP.
A karshen makon jiya aka ga Isa Ali Ibrahim Pantami a gidan tsohon gwamnan Jigawa wanda ya yi yunkurin zama shugaban PDP a 2026.

Source: Facebook
Isa Pantami sun ziyarci Sule Lamido
Muhammad Umar Danmasani ya yi amfani da shafin Facebook, ya daura cikakken jawabin da ‘dan takarar gwamnan jihar Gombe ya yi a Jigawa.
Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami wanda ya fara da Bismillah da neman tsari daga shaidan, ya kira Sule Lamido da baba, shugaba kuma jagoransu.
Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamanin ya fara da gode wa shugabannin jam’iyya, ‘yan takara da kuma abokan siyasa daga jihohi.
Yadda Isa Pantami yake mutunta Sule Lamido
Pantami ya ce ba komai ya kawo su garin Bamaina ba illa mutuntawa, karramawa da girmama Sule Lamido wanda ya yi gwamna sau biyu a baya.
Da farko an yi niyya za a hadu da Alhaji Sule a Abuja ne, amma sai ya fada masu cewa a garinsa na Bamaina ne yake karbar baki irin wannan.
“Mai girma a matsayin uba muke daukarsa, gabanin a yi komai a rayuwa , wanda aka ce uba ne, a al’adar shi ne an kai shi makura na girmamawa.
"Da siyasa ko babu, da mukami ko babu, a ko ina mu ka gan shi, to baba mu ka gani. Kuma yana da hakkin a ba shi matsayi na uba a ko ina yake."
- Sheikh Isa Ali Pantami
Isa Pantami a kan dalilin zuwa Bamaina
Malamin ya ce samun irinsu Sule a wuri albarka ne ganin shekarunsa da kuma mukaman da ya rike.
A koyaushe babba ya yi magana, ana daukar darashi a cewar Pantami, ya ce saboda haka ne suka ziyarci dattijon mai neman cika shekaru 78 a duniya.
Saboda gwagwarmaya da fadi-tashin tsohon ministan harkokin wajen, Pantami ya ce daga kalaman mutane kamarsa za a samu ilmin da bai cikin littafi.
“Duk inda mu ke da dattawa, kusantar su alheri ne. A minti biyar ko 10, sai a yi bayanin da zai amfane ka har karshen rayuwarka.”
- Isa Ali Pantami
Abu na uku da ya fada kuwa shi ne, da yawansu suna kaunar Sule saboda son talakawa, ya ce an ga yadda suka amfana a mulkinsa daga 2007 zuwa 2015.
Pantami ya ce Alhaji Sule ya aro wannan akida ne daga tsohon jagoransu Malam Aminu Kano.
Ban da ayyuka musamman a bangaren ilmi da ya narka da yake gwamna, Sheikh Pantami ya ce kaunar talakawa ce take sa Sule yake zuwa Bamaina.
Wasu mahalarta taron gidan Sule Lamido
Cikin mahalarta taron na manyan PDP akwai tsohon shugaban ‘yan sanda, Suleiman Abba da shugaban PDP na Jigawa, Babande Ibrahim.
Legit Hausa da ta saurara ta ji Majidadin Daular na Usmaniya ya kira Santurakin Dutse mai takarar gwamnan Jigawa PDP da ‘danuwa kuma kaninsa.
A karshe ya rufe da yi masa addu’ar ya gama lafiya kuma ya ji kan mahaifansa da suka rasu.
Ga bidiyon nan a shafin wata gidauniyar Pantami a Facebook
Sule ya tuna wa Pantami tsohuwar maganarsa
Labarin da aka samu jiya ya ce tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi wa Farfesa Isa Ali Pantami shagube lokacin da suka hadu a gidansa.
Babban 'dan siyasar ya tunatar da shi yadda ya taba kiran jam'iyyar PDP da "jam'iyyar kafirai" a shekarun baya lokacin yana wa'azi a jami'ar ATBU.
Sule ya fadi hakan ne yayin da ya karbi bakuncin 'yan takarar gwamna na jam'iyyar PDP daga jihohin Gombe, Bauchi, Kano, Yobe, da Jigawa a gidansa.
Asali: Legit.ng


