Ran Rarara Ya Baci da Aka Soki Tinubu kan Tsaro, Ya Zargi Davido da Bata Najeriya
- Babban mawakin da ke yi wa jam'iyyar APC waka, Dauda Kahutu Rarara ya yi magana game da rashin tsaro da ya addabi tarayyar Najeriya
- Rarara ya magantu ne bayan fitaccen mawakin Najeriya da aka fi sani da Davido ya nuna sunayen daliban Oyo da aka sace a Amurka
- Dauda Kahutu ya nuna rashin jin dadi game da abin da Davido ya yi, yana cewa hakan zubar da mutuncin Najeriya ne a idon duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Yayin da ake cigaba da magana game da zafafa hare-hare da 'yan bindiga suke yi a Najeriya a kwananan nan, mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara ya yi magana.
Rarara ya nuna takaici kan yadda mawakin Najeriya, David Adedeji Adeleke da aka fi sani da Davido ya nuna matsalar tsaron Najeriya a wajen bikin kofin duniya a Amurka.

Source: Facebook
Dauda Kahutu ya yi magana ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya yi martani game da abubuwa da dama.
Maganar Dauda Rarara kan rashin tsaro
A bayanin da ya yi, Dauda Kahutu ya nuna cewa zuwa wajen gasar kofin kwallon kafa duniya a nuna sunayen dalibai da malaman da aka sace a Oyo bai dace ba.
Ya bayyana cewa abin da Davido ya yi tamkar kunce wa Najeriya zani a kasuwa ne maimakon tallafawa kasar wajen magance rashin tsaro.
Rarara ya ce:
'Ya za ka dauki sirrin Najeriya, sirrin mu na cikin gida ka dauka ka kai mana duniya. Me za ka samu?"
Mawakin ya bayyana cewa duk masu irin halin Davido su ne masu mayar da kasar baya wajen magance matsalar tsaron Najeriya.
Rarara ya zargi Davido da ta'addanci
Rarara ya kalubanci Davdo da cewa bai san dalilin sace yaran da aka yi ba, inda ya ce 'yan ta'addan sun sace yaran ne domin a saki sauran manyan masu garkuwa da aka tsare.

Kara karanta wannan
Tinubu zai kashe Naira tiriliyan 5 kan tsaro, za a dauki sababbin ƴan sanda 50000
Duk da haka, Rarara ya ce gwamnati ta ki sakin 'yan ta'addan da aka kama ta sha alwashin sai ta ceto dalibai da malaman da aka sace.
"Ni a tunani na yanzu ma, Davido dan Ansaru ne, dan ta'adda ne. Saboda wannan babban ta'addanci ne, ya ma kasar mu ta'addanci. Ya dauki sirrin kasar ya kai. Kuma karya ya ke ya sani."

Source: Facebook
Rahoton Challens TV ya nuna cewa Davido ya sanya riga mai dauke da sunayen 'yan makaranta da aka sace yayin da ya yi waka a wajen taron bude gasar kofin duniya ta bana na 2026.
Buratai ya yi gargadi kan tsaro
A wani rahoto, kun ji cewa tsohon hafusn sojin kasa na Najeriya, Janar Tukur Buratai (mai ritaya) ya yi gargadi kan matsalar tsaro da ta yi katutu a kasar nan.
Ya bayyana cewa idan ba a dauki matakan da suka dace ba, masu garkuwa da mutane za su fara kai hari kan manyan shugabannin Najeriya.
Maganar Buratai na zuwa ne bayan tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Janar Rabe Abubakar (Mai ritaya) ya rasu a hannun 'yan ta'adda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
