PDP Ta Yi Kaca Kaca da Gwamnatin Gombe kan Zargin bai wa Mawakin Kano N315m
- Jam'iyyar PDP a jihar Gombe ta zargi gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da bayar da miliyoyin Naira da filaye akalla hudu ga wani mawaki daga jihar Kano
- Jam'iyyar adwa ta PDP ta ce ya dace a karkata wannan kudi zuwa ilimi, lafiya, noma, matasa da sauran ayyukan ci gaban jama'a a sassa daban-daban na jihar Gombe
- PDP ta bukaci gwamnatin Muhammadu Inuwa na jihar Gombe ta fito ta yi bayani kan dalilin bayar da tallafin da kuma rabon filayen domin tabbatar da gaskiya da rikon amana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Gombe – Jam'iyyar PDP reshen jihar Gombe ta caccaki gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya kan zargin amincewa da bayar da tallafin da ya kai Naira miliyan 315 tare da filaye hudu ga wani fitaccen mawaki daga jihar Kano.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran PDP na jihar, Abdulkadir Ahmad Dukku, ya fitar, jam'iyyar ta ce ta samu sahihan bayanai da ke nuna cewa gwamnatin jihar ta amince da kashe Naira miliyan 115.

Source: Facebook
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa an yi amfani da kudin ne domin sayen motar Toyota Coaster ga mawakin, baya ga ba shi tallafin kudi na Naira miliyan 200.
PDP ta soki gwamnan Gombe
Sahara Reporters ta ruwaito cewa PDP ta bayyana cewa jimillar kudin da ake zargin an ware wa mawakin ta kai Naira miliyan 315.
Jam'iyyar adawar ta nuna cewa wannan mataki ya zo ne a lokacin da jihar Gombe ke fuskantar kalubalen ilimi, inda ta ce akwai yara 787,619 da ba sa zuwa makaranta.
A cewarta, da an karkata wannan adadi na kudi zuwa shirye-shiryen ilimi, da za a taimaka wajen dawo da dubunnan yara makaranta, tare da inganta bangarorin kiwon lafiya da sauran muhimman ayyukan gwamnati.

Source: Original
Har ila yau, PDP ta yi zargin cewa gwamnatin jihar ta bai wa wannan mawaki filaye hudu a Shehu Abubakar District Layout, lamarin da ta ce ya jawo damuwa.
Jam'iyyar ta ce yankin ya kasance cikin wadanda aka soke ko rage girman filayensu a wani shirin gwamnatin jihar ba tare da biyan diyya ga masu filayen ba.
Bukatar PDP ga gwamnatin APC
PDP ta bukaci gwamnatin jihar Gombe ta fito ta bayyana hujjar da ta dogara da ita wajen bayar da kudin da filayen, tana mai cewa al'umma na da hakkin sanin yadda ake amfani da dukiyar gwamnati.
A cikin sanarwar, PDP ta ce irin wannan kashe kudi ya tayar da tambayoyi kan fifikon gwamnatin jihar, tana mai cewa da wannan kudi za a iya aiwatar da tsare-tsaren da za su amfanar da dubban mazauna Gombe.
Jam'iyyar ta kara da cewa za ta ci gaba da fafutukar ganin an tabbatar da gaskiya, rikon amana da amfani da dukiyar al'umma yadda ya kamata domin ci gaban jihar.
PDP da ADC sun fadi zabe a Gombe
A baya, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta a Gombe, GOSIEC ta bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi da aka yi jihar Gombe, inda jam'iyya mai mulki ta APC ta yi nasara.
An gudanar da zaben ne a yau Asabar 27 ga watan Yunin 2026 na kujerun shugabannin kananan hukumomi 24 da kujerun kansiloli 240 inda wani masoyin Farfesa Isa Ali Pantami kuma dan PDP ya yi fatali da zaben.
Mohammed Babayo Pantami ya yi fatali da maganar gudanar da zaben da jam'iyyu shida ne suka tsayar da 'yan takara a zaben shugabannin kananan hukumomi, ciki har da APC, Youth Party, NRM, ZLP, AAC da DLA.
Asali: Legit.ng


