Peter Obi Ya Nuna Damuwa kan Gargadin da Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi wa Arewacin Najeriya

Peter Obi Ya Nuna Damuwa kan Gargadin da Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi wa Arewacin Najeriya

  • Peter Obi ya nuna damuwa kan gargadin da Majalisar dinkin duniya ta yi game da karuwar yunwa a tsakanin al'umma a Arewacin Najeriya
  • Dan takarar shugaban kasa na NDC ya bukaci gwamnatocin tarayya da na jihohi su tashi tsaye wajen inganta harkokin noma da samar da tsaro
  • Obi ya ce rashin tsaro, ciki har da hare-haren 'yan bindiga da masu tayar da kayar baya, ya hana manoma damar komawa gonakinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi, ya nuna damuwa kan sabon gargadin Majalisar Dinkin Duniya game da karuwar matsalar yunwa a Arewacin Najeriya.

Ya ce lamarin abin damuwa ne musamman ganin cewa Arewacin Najeriya ne aka fi sani da kasancewa cibiyar noman abinci ta kasar.

Kara karanta wannan

Rahoton IMF: Atiku ya aika tambaya ga Tinubu kan 'wanda ke sace 2%' na kuɗaɗen Najeriya

Peter Obi.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Peter Obi, tsohon gwamnan Jihar Anambra, ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar, 4 ga watan Yuli, 2026.

Obi ya bukaci gwamnati ta kara himma

Peter Obi ya ce akwai bukatar gwamnati ta aiwatar da ingantattun manufofi domin dakile tabarbarewar matsalar jin kai da ke kara kamari.

Ya bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su zuba jari wajen tabbatar da tsaron yankunan noma tare da tallafa wa kananan manoma da kayan aiki da sauran abubuwan da za su taimaka musu.

Haka kuma ya bukaci gwamnatoci su yi aiki kafada da kafada da Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) da sauran abokan hulda domin cike gibin kudaden da ake bukata kafin matsalar ta kara tsananta.

Mutum miliyan 17 na fama da yunwa

A cewar Obi, sabon rahoton WFP ya nuna cewa fiye da mutum miliyan 17 a jihohi tara na Arewacin Najeriya na fama da matsananciyar yunwa.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta shiga batun ma'aikatar bogi, ta aika sako ga gwamnatin Tinubu

Ya kara da cewa sama da mutum miliyan 35 a fadin Najeriya na iya shiga cikin hadarin karancin abinci a wannan lokacin da ake fama da karancin amfanin gona.

Abin da ya jawo karancin noma a Arewa

Obi ya ce rashin tsaro, ciki har da hare-haren 'yan bindiga da masu tayar da kayar baya, ya hana manoma da damar komawa gonakinsu.

A cewarsa, wannan na daga cikin manyan matsalolin da ke hana karuwar samar da abinci a kasar.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a taron da ya halarta a kasar Ruwanda Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Saboda haka ya bukaci a kara inganta tsaro a yankunan noma tare da kara zuba jari wajen bunkasa ababen more rayuwa a karkara da kuma habaka ayyukan noma.

Tsohon gwamnan ya kuma yi kira ga masu tsara manufofi su fifita tsare-tsaren tattalin arziki da za su kara yawan noman kasa da kuma bunkasa masana'antun da suka shafi noma.

Peter Obi ya fara yiwa Najeriya tanadi

A wani labarin, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana tanadinsa na gina Najeriya mai albarka da ci gaba idan ya samu nasara a 2027.

Obi ya tuna cewa tun lokacin da ya fara neman shugabancin ƙasa ya yi alƙawarin ɗora Najeriya kan turbar haɗin kai da sauyi mai ɗorewa.

Ya ce manufarsa ta ta'allaka ne kan haɗa kan al'umma, tabbatar da adalci, daidaito da bai wa kowane ɗan ƙasa damar cimma burinsa ta hanyar da doka ta tanada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262