Bayan an Shafe Shekaru ba ko Digo, Gwamnati Ta Farfaɗo da Matatar Ruwa a Kano
- Gwamnatin jihar Kano ta sake share hawayen wasu daga cikin mazauna karkara da ke fama da rashin ruwan famfo saboda lalacewa matatar ruwa
- Kwamishinan Albarkatun Ruwa Dr. Dahir M. Hashim ya sanar da cewa al'ummomi za su fara karbar ruwa tun ranar Talata ta 8 ga Yuli 2026 bayan gyaran da ake yi
- Ya sanar da cewa an sanya sabon injin lantarki na 800 kVA kuma an gyara injunan fitar ruwa a matsayin wani bangare na gyaran tsarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Mazauna yankunan karkara da ke kananan hukumomi biyu a jihar Kano sun samu tagaomashin gwamnatin Abba Kabir Yusuf bayan an fara tura masu ruwa.
Wannan na zuwa ne bayan gwamanti ta gyara matatar ruwa ta Guzu-Guzu, wanda ya tsaya da aiki na tsawon shekara hudu babu ko digon ruwa.

Source: Facebook
A sanarwar da Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dahir M Hashim ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya tabbatar da cewa an gyara matatar mai karfin samar da lita miliyan 7.2 na ruwa a kowace rana.
An gyara matatar ruwa a jihar Kano
A cikin sakon, Kwamishinan ta bayyana cewa wannan matata da ta farfado daga dogon suman da ta yi za ta samar da ruwa ga mazauna kananan hukumomin Kabo da ta Rimin Gado.
Dr. Dahir M. Hashim, ya ce gyara matatar wani babban mataki ne a kokarin gwamnati na tabbatar da samun ruwan sha mai tsafta ga al'umma.
A cewar kwamishinan, al'ummomi da ke karkashin wannan tsarin za su fara karbar ruwa tun ranar Laraba, 8 ga Yuli 2026, yayin da ake ci gaba da gwaje-gwaje da kaddamar da tsarin daki-daki.
An sanya sabon injin lantarki mai karfin 800 kVA, da gyaran injunan fitar ruwa daga guda hudu, da kuma sabunta ginin da ake sarrafa injuna a ciki, ofisoshin ma'aikata da wuraren tsaro. Kwamishinan ya kara da cewa za a ci gaba da aiki har sai an kai matakin biyan bukatun mazaunan yankunan da ke amfana da shi.
Gwamnatin Kano ta jaddada alkawarinta
Dr. Hashim ya jaddada cewa dawowar aikin tsarin Guzu-Guzu ta nuna sadaukarwar gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen maido da muhimman ababen more rayuwa na ruwa a duk fadin jihar.

Source: Facebook
Ya ce gudanarwar Gwamna Abba Kabir Yusuf yana kokarin gyara dukkanin wuraren samar da ruwa guda 19 da ke jihar Kano, domin tabbatar da ruwan sha mai tsafta ga kowa da kowa. A makonni da suka wuce, gwamnatin jihar ta kuma fara gyaran matatar ruwa na yanki na Joda, wanda ya tsaya aiki tsawon shekara bakwai, kuma ta sake fara aika ruwa da aka tsarkake daga tashar Challawa zuwa Goron Dutse.
'Yan Tijjaniya sun goyi bayan gwamnan Kano
A wani labarin, kun ji rahotanni sun nuna cewa majalisar shura ta 'dariƙar Tijjaniyya ta ayyana goyon bayanta ga tazarcen gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a zaben 2027 bayan sun cimma matsaya.
A wani taron da ta yi, majalisar ta ce ta yanke shawarar ne saboda abin da ta bayyana a matsayin nagartaccen shugabancin da Abba Kabir ya nuna musamman wajen kawo ayyukan ci gaba a fadin jihar.
A na shi bangaren, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa shugabannin majalisar bisa addu'o'i da goyon bayan da suke cigaba da ba si a jihar Kano tare da jaddada kudurinsa na kawo ci gaba mai dorewa.
Asali: Legit.ng

