Ministan Tsaro: Abin da Ya Hana Sojoji Gwabza wa da Ƴan Bindiga don Ceto Ɗaliban Oyo
- Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya ya ce 'yan bayyana dalilin da ya hana jami'ai su fafata da yan bindiga da suka yi garkuwa da daliban jihar Oyo
- A makonnin da suka wuce, yan bindiga sun shiga jihar inda suka yi awon gaba da dalibai da malamansu a makarantu daban-daban na Oyo, aka nutsa da su cikin daji
- Da ya ke bayani a kan dalilin da ya sa har yanzu aka gaza ceto su, Christopher Musa ya bayyana cewa akwi dalili, kuma ana bakin kokari wajen kwato lafiya lau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa 'yan bindigar da suka sace dalibai da malamai a jihar Oyo sun yi barazanar kashe duk wadanda suke tsare da su.
Sun yi wannan barazana ne tare da bayyana cewa jami'an tsaro su tsaya a inda su ke, domin idan suka farmaki maboyarsu, a bakin rayukan yaran.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa Janar Christopher Musa ya bayyana cewa masu garkuwar sun yi amfani da daliban da malaman a matsayin hanyar matsa lamba domin tilasta gwamnati ta sako wasu manyan kwamandojinsu da ke tsare a hannun sojoji.
Sojoji suna kokari - Christopher Musa
Jaridar The Cable ta kawo labarin cewa Janar Christopher Musa mai ritaya ya bayyana cewa jami'an tsaro suka shirya daukar mataki domin ceto wadanda aka sace.
Sai dai tuni 'yan bindigan suka yi gargadin cewa za su kashe dukkannin yaran idan dakarun suka kara matsowa kusa da maboyarsu.
Ministan ya bayyana cewa bayanan sirri da hukumomin tsaro suka tattara sun nuna cewa manufar masu garkuwar ita ce su yi ciniki da rayuwar daliban domin a sako shugabanninsu da ke tsare.
Christopher Musa ya nemi a kashe yan bindiga
Da yake magana kan hanyoyin da gwamnati za ta bi wajen dakile ayyukan 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane, Christopher Musa ya ce lokaci ya yi da za a tsaurara hukunci kan masu aikata irin wadannan manyan laifuka.

Source: Facebook
A cewarsa, dokokin da ake da su a yanzu ba su da tsauri sosai, lamarin da ke sa masu aikata laifuffuka su ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da tsoron hukunci mai tsanani ba.
Ministan ya ce samar da hukunci mai tsauri, ciki har da hukuncin kisa ga wadanda aka samu da laifin garkuwa da mutane da ta'addanci, zai iya zama babban abin tsoratarwa da zai rage yawaitar irin wadannan laifuffuka.
Umarnin Christopher Musa ga sojoji
A wani labarin, mun wallafa cewa Ministan tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya ya ba jami'an tsaro izini su harbe 'yan bindiga da 'yan ta'adda nan take ba tare da jiran wani umarni daga sama ba.
Janar Christopher Musa ya ce duk jami'in da ya ki daukar mataki zai fuskanci hukunci kamar mai hada baki da 'yan ta'addar da ke kashe-kashe da hana al'umma jin dadin rayuwarsu yadda ya dace.
Ya bayyana haka ne yayin da gwamnatin jihar Sakkwato ta kaddamar da motocin sulke da kayan tsaro na sama da Naira biliyan 27 domin yaki da rashin tsaron da suke fama da shi a yankuna da dama.
Asali: Legit.ng

