An Rantsar da Sabon 'Dan Majalisar Tarayya daga Jihar Kano, Ya Maye Gurbin Wanda Ya Rasu

An Rantsar da Sabon 'Dan Majalisar Tarayya daga Jihar Kano, Ya Maye Gurbin Wanda Ya Rasu

  • Majalisar Wakilai ta tarayya ta rantsar da Hon. Shuaibu Rabiu bayan nasarar da ya samu a zaɓen cike gurbin da aka gudanar a Kano
  • Hon. Shuuaibu Rabiu ya zama ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Dawakin Kudu/Warawa ta jihar Kano a ƙarƙashin APC
  • Hukumar INEC ta gudanar da zabe ne bayan rasuwar Muhammad Danjuma-Hassan na jam'iyyar NNPP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Majalisar Wakilai ta Tarayya ta rantsar da sabon mamba, Shuaibu Rabiu, a matsayin ɗan majalisa da zai wakilci mazabar Dawakin Kudu/Warawa ta jihar Kano.

Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ne ya jagoranci rantsar da Shuaibu Rabiu tare da karɓarsa a hukumance cikin mambobin Majalisa ta 10.

Majalisa.
Yan Majalisar wakilai na tsakiyar zama a zauren Majalisar tarayya da ke Abuja Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Ya maye gurbin Danjuma Hassan

Premium Times ta ce rantsar da sabon ɗan majalisar na zuwa ne makonni kaɗan bayan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gudanar da zaɓen cike gurbi domin maye gurbin kujerar da ta zama babu kowa.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda na barazana a iyakokin Najeriya, sojoji sun shirya murkushe su

Kujerar ta zama babu mai riƙe da ita ne bayan rasuwar tsohon ɗan majalisar mazabar, Muhammad Danjuma-Hassan, wanda ya kasance ɗan jam'iyyar NNPP.

Sashe na 76(2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ya tanadi cewa INEC ta gudanar da zaɓen cike gurbi idan kujerar Majalisar Tarayya ta zama babu kowa a kanta fiye da watanni uku kafin ƙarshen wa'adin majalisar.

An tsara wannan doka ne domin tabbatar da cewa al'ummomin da abin ya shafa ba su rasa wakilci na tsawon lokaci ba.

APC ta yi nasara da tazarar ƙuri'u

INEC ta gudanar da zaɓen cike gurbin ne a ranar 20 ga Yunin 2026, inda Shuaibu Rabiu, ɗan takarar jam'iyyar APC, ya samu nasara, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, Baturen Zaɓe, Umar Sani, ya ce Shuaibu Rabiu ya samu ƙuri'u 35,356, wanda ya ba shi damar kayar da sauran 'yan takarar.

A sakamakon da aka fitar, Lawal Garba-Haruna na jam'iyyar APM ya zo na biyu da ƙuri'u 268, yayin da Abubakar Yahaya-Muhammad na jam'iyyarbLP ya samu ƙuri'u 98.

Kara karanta wannan

Ahmad Lawan: Kotu ta ba da umarni kan shari'ar neman hana sanatan tikiti

Mazabar Kano ta sake samun wakilci

Da wannan rantsuwa, Shuaibu Rabiu zai fara cikakken aiki a Majalisar Wakilai, ciki har da halartar zaman majalisa, shiga kwamitoci da kuma muhawara kan kudurori da dokoki.

Hakan ya kawo ƙarshen gibin wakilci da al'ummar Dawakin Kudu da Warawa suka fuskanta tun bayan rasuwar Muhammad Danjuma-Hassan.

Rikici ya barke a Majalisar wakilai

A wani rahoton, kun ji cewa an hargitse a zaman majalisar wakilai da aka gabatar da bukatar a gayyaci Shugaba Bola Tinubu ya yi bayani kan jinkirin aiwatar da kasafin 2025.

'Yan majalisar sun samu sabani kan wani kudiri da ke neman a gayyaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, matakin da mambobin APC suka nuna sam ba su yarda ba.

Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya dauki lokaci kafin ya kwantar da hankulan 'yan majalisar, yana mai bayyana cewa batutuwan da aka gabatar karkashin batu na gaggawa ba sa bukatar muhawara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262