Yadda Aka Ware N400bn na Gyaran Masallatai, Masarautu a Kasafin Kudin 2026
- Rahotanni sun bayyana wasu makudan kudi da aka ware a kasafin kudin shekarar 2026 saboda gyaran masallatai, masarautu
- Masana sun soki yadda aka ware kuɗaɗe masu yawa ga ƙananan ayyuka, suna cewa hakan na rage zuba jari a lafiya, ilimi, tsaro
- Rahoton ya kuma nuna wasu ayyukan da aka saka cikin kasafin ba su da alaƙa da aikin wasu hukumomi, lamarin da ya jawo suka kan tsarin kasafi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wasu rahotanni sun bankado yadda aka ware biiyoyin Naira domin gyaran masallatai, masarautu da dakunan taro a kasafin kudi.
Binciken ya nuna cewa ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnatin tarayya guda 78 sun ware kusan naira biliyan 400 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026.

Source: Twitter
Musabbabin ware N400bn a kasafin kudi
Rahoton Punch ya ce an ware kudin ne domin gina da gyaran dakunan taro, masallatai, fadodin sarakunan gargajiya, kasuwannin ƙauyuka da cibiyoyin al’umma.
Fiye da rabin wannan kuɗi an ware shi ne domin ayyukan da masana suka ce ba su da muhimmancin ci gaba kai tsaye.
Waɗannan sun haɗa da rabon hatsi, babura, keken adaidaita sahu, tallafa wa ƙungiyoyin ajiya da kuma gina gidajen tarihi da ƙananan filayen wasa.
Daga cikin hukumomin da binciken ya shafa akwai Hedikwatar Ma’aikatar Tsaro, Rundunar Sojin Sama, Kwalejin Tsaro ta Najeriya, Ma’aikatar Yaɗa Labarai, da wasu cibiyoyin bincike da ilimi da ke sassa daban-daban na ƙasar.
Sauran hukumomin sun haɗa da Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Cibiyar Binciken Masana’antu ta Oshodi, Cibiyar Binciken Gine-gine da Hanyoyi, da wasu cibiyoyin bincike da horo na aikin gona da haɗin gwiwa.

Source: UGC
Martanin masana tattalin arziki kan lamarin
Masana sun bayyana cewa irin waɗannan ayyuka ba su dace da manyan buƙatun Najeriya ba, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar ƙalubalen tattalin arziki, cewar Tribune.
A cewarsu, rarraba kuɗi zuwa ƙananan ayyuka masu ƙarancin tasiri yana hana gwamnati aiwatar da manyan tsare-tsaren ci gaba, tare da raunana da’a wajen gudanar da kasafin kuɗi da ingancin ayyukan gwamnati.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: An hango yadda malaman makaranta masu yawa za su ajiye aiki a Borno
Rahoton ya kuma nuna cewa an saka wasu ayyuka cikin kasafin hukumomin da ba su da alaƙa da aikinsu. Misali, Cibiyar Binciken Gine-gine da Hanyoyi ta samu ayyukan gina dakunan taro, kasuwanni, fadodin sarakuna da gyaran masallatai a jihohi daban-daban.
Haka kuma, Cibiyar Haɓaka Ƙwazo ta Ƙasa ta samu ayyuka irin su tallafa wa mawaƙan Ijaw, gina fadar sarki, gyaran fadodin sarakuna da gina mayanka, yayin da Cibiyar Lissafi ta Ƙasa za ta tallafa wajen gina sashen ilimin zamantakewa a Jami’ar Ahmadu Bello.
Rahoton ya tuna cewa Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2026 mai jimillar Naira tiriliyan 68.32, yayin da har yanzu ake ci gaba da aiwatar da wasu sassan kasafin shekarar 2025.
Gyaran gasarautu: Atiku ya dura kan Tinubu
An ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kalubalanci gwamnatin Tarayya kan ware biliyoyi saboda masarautu.
Ya ce kundin tsarin mulkin 1999 bai ba gwamnatin Tarayya ikon kula ko daukar nauyin cibiyoyin gargajiya ba, sai gwamnatocin jihohi kawai.
Atiku ya bukaci a bayyana jerin fadojin, wurarensu, kudaden da aka ware, tsarin bayar da kwangila da hujjar kundin tsarin mulki kan aikin.
Asali: Legit.ng
