'Dalilin da Ya Sa Atiku ba Zai Yi Nasara ba a Zaben Shugaban Kasa Na 2027'
- Tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, ya yi tsokaci kan takarar da Atiku Abubakar zai yi ta neman kujerar shugaban kasa a zaben 2027
- Ali Modu Sheriff ya bayyana cewa Atiku Abubakar yana yin kidansa da rawarsa ne kawai shi kadai domin ba zai kai labari ba a zaben
- Tsohon gwamnan ya jaddada cewa lokaci bai yi ba da yankin Arewacin Najeriya zai sake samar da shugaban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Borno kuma jigo a jam'iyyar APC, Ali Modu Sheriff, ya yi watsi da damar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Ali Modu Sheriff ya jaddada cewa yanzu ba lokacin Arewa ba ne na fitar da shugaban kasa na gaba a Najeriya.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan na jihar Borno ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin 'Politics Today' na tashar Channels tv a ranar Litinin, 6 ga watan Yulin 2026.
Meyasa Atiku ba zai yi nasara ba?
Ali Modu Sheriff ya ce Arewa ba za ta marawa burin Atiku na zama shugaban kasa baya ba saboda lokaci ne na dan Kudu.
A cewarsa, shugabannin siyasar Najeriya sun cimma matsaya bayan yakin basasa domin tabbatar da daidaiton shiyyoyi a shugabancin kasar.
“Bayan yakin basasa, shugabanninmu sun ce ba za a sake samun wannan yanayi ba a Najeriya, akwai yarjejeniyar shiyyoyi. Shi kuwa Atiku, wannan ba lokacinmu ba ne yanzu. Shi kadai yake kidansa yake rawarsa saboda lokaci ne na Kudu. Buhari ya gama shekaru takwas kwanan nan."
“Idan Atiku yana son zama shugaban kasa zai iya jira, shi jagora ne a Arewacin Najeriya, kuma ya cancanta kwarai da gaske, amma wannan ba lokacinmu ba ne yanzu, sai ya jira har zuwa shekarar 2031. Wancan shi ne lokacin Arewa, a halin yanzu, lokaci ne na Kudu.”
- Ali Modu Sheriff
Ya nuna kwarin gwiwa kan tazarcen Tinubu

Kara karanta wannan
"Yana son raba Najeriya"; Sheriff ya soki Peter Obi kan neman Tinubu ya yi murabus
Sheriff ya nuna kwarin gwiwar cewa Shugaba Tinubu zai samu nasarar yin tazarce a shekarar 2027, amma ya ce APC ba za ta dauki komai da wasa ba kuma za ta yi aiki tukuru gabanin zabubbukan.
Tsohon gwamnan na Borno ya kuma yi watsi da burin shugabancin kasa na tsohon dan takarar jam'iyyar LP, Peter Obi, wanda ke neman shugaban kasa a shekarar 2027 a karkashin sabuwar jam'iyyar NDC da aka yi wa rajista.
A cewarsa, Peter Obi wanda ya samu kuri'u sama da miliyan shida inda ya zo na uku a zaben shugaban kasa na shekarar 2023, ba zai samu goyon bayan masu jefa kuri'a na Arewa ba a shekarar 2027.

Source: Facebook
Ana son Atiku ya sauya Amaechi
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kungiya mai suna Southern Political Progressives Amalgamation Forum (SPPAF), ta mika bukatarta ga Atiku Abubakar.
Kungiyar na son a cire tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi daga matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ADC.
a gargadi tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da kada ya tafi da Amaechi a matsayin mataimakinsa a zaben 2027.
Asali: Legit.ng
