Segalink Ya Yi Maganar da ka Iya Zama Barazana ga Takarar Peter Obi da Kwankwaso a 2027

Segalink Ya Yi Maganar da ka Iya Zama Barazana ga Takarar Peter Obi da Kwankwaso a 2027

  • An fara hasashen cewa dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi bai cancanci ya zama shugaban Najeriya ba
  • Dan gwagwarmaya kuma mai sharhi kan al'amuran al'umma, Segun Awosanya ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi
  • Ya kuma bayyana cewa a baya ya yabi Peter Obi ne saboda wasu kalamai masu kyau da ya yi kan yadda za a gyara rayuwar talakan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Mai sharhi kan harkokin al'umma kuma ɗan gwagwarmaya, Segun Awosanya, ya bayyana abin da ya sa yake ganin Peter Obi ba zai taba mulkin Najeriya ba.

Segun Awosanya, wanda aka fi sani da Segalink, ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC ba shi da halayen da suka dace domin jagorantar Najeriya.

Kara karanta wannan

Komai zai fito: APC na shirin fitar da bayanan mataimakin Tinubu a 2027

Obi .
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Segalink ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin Politics Hub na Vanguard, inda ya yi magana kan halin da ƙasa ke ciki, babban zaɓen 2027 da kuma burin Peter Obi na zama shugaban ƙasa.

Dalilin da zai hana Obi mulkin Najeriya

A cewarsa, tsohon gwamnan jihar Anambra ya gina farin jininsa ne ta hanyar amfani da fushin jama'a maimakon nuna nagartaccen shugabanci.

Ya ce:

"A bayyane yake ga kowa cewa mutumin da yake nuna kansa ta wata fuska alhali a zahirin gaskiya ba haka yake ba, ya kamata a tona ainihin halayensa.
"A ganina, Peter Obi shugaban taron jama'a ne kawai, wanda yake anfani da fushin mutane wajen ɓata sunan wasu da kuma matsa musu domin ya samu karɓuwa, sannan ya yi anfani da hakan wajen neman mulki."

Ya musanta rikici da Obidients

Da aka tambaye shi ko sukar da yake yi wa Obi ta samo asali ne daga rashin jituwa da magoya bayansa, Segalink ya ce ba shi da wata matsala da ƙungiyar Obidient.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Jonathan ya wanke kansa kan zargin karɓo N500bn don raba ƙuri'ar Obi

Ya ce:

"Ba ni da wata matsala da kowa. Ko ma ba na kallonsu a matsayin wani abu. Ina mayar da hankali ne kan abin da nake yi."
Segalink.
Dan gwagwarmaya, Segun Awosanya, wanda aka fi sani da Segalink Hoto: Segun Awosanya
Source: Facebook

Dalilin Segalink na yabon Obi a baya

Segalink ya kuma bayyana dalilin da ya sa a baya ya taɓa yabon Peter Obi, yana mai cewa hakan bai kasance tallata shi ba.

Ya ce:

"A baya na fito na yaja wa Peter Obi ne saboda a wancan lokacin yana magana ne kan matsalolin da suka shafi masu ƙaramin karfi a cikin al'umma."

Ya ce yabon nasa wata fahimta ce ta abin da Obi yake faɗa a lokacin, ba wai yana goyon bayan siyasarsa ba, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.

Obi ya bukaci Tinubu ya yi murabus

A wani rahoton, kun ji cewa ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya sake jaddada bukatarsa ta cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya nuna damuwa kan gargadin da Majalisar ɗinkin duniya ta yi wa Arewacin Najeriya

Peter Obi ya kafa hujja da cewa sabon bayanin da asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya fitar game da kashe kudaden da ba su cikin kasafin kudin Najeriya.

Ya ce bayanin na IMF ya kara tabbatar da damuwar da ake da ita kan rashin rikon amana, cin hanci da rashawa, da kuma yadda ake gudanar da kudaden kasar a karkashin gwamnati mai ci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262