2027: Malami Ya Yi Hasashen Yadda Za Ta Kaya tsakanin Atiku, Tinubu da Obi

2027: Malami Ya Yi Hasashen Yadda Za Ta Kaya tsakanin Atiku, Tinubu da Obi

  • Limamin cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa takarar shugaban kasa ta 2027 za ta fi karkata tsakanin Tinubu da Atiku
  • Ayodele ya ce Peter Obi zai fuskanci kalubale a Arewa, yana kuma ikirarin cewa za a tauye masa kuri'u a wasu sassan Najeriya
  • Malamin ya ce Kano da Abuja za su kasance wuraren fafatawa mai zafi, yana mai cewa babu dan takarar da zai samu cikakkiyar nasara a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lagos - Jagoran cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashe game da zaben shugaban kasa a 2027.

Malamin cocin ya ce za a fafata sosai a zaben shugaban kasa tsakanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.

An yi hasasehen zabe tsakanin Atiku da Tinubu da Obi
Shugaba Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi. Hoto: Bayo Onanuga, Atiku Abubakar, Peter Obi.
Source: Facebook

Ayodele ya bayyana hakan ne a cikin sabon littafinsa mai taken 'Warnings To The Nations 2026/2027 Edition', wanda aka kaddamar ranar Asabar, 4 ga Yulin 2026, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Da gaske alkalin da ya ba Tinubu nasara a kotu a zaben 2023 ya makance?

Fasto ya yi hasashe kan zaben 2027

Littafin mai shafuka 405 ya kunshi hasashe kan batutuwan Najeriya da na duniya, malamin ya kuma yi ikirarin cewa Peter Obi zai fuskanci kalubale a yankin Arewa.

Ya kara da cewa Obi zai yi wahala wajen samun nasara a Arewa, sannan ya yi zargin cewa za a tauye masa wasu kuri'u a wasu sassan kasar.

Ayodele ya ce Peter Obi zai yi gwagwarmaya a Arewa, yayin da Bola Tinubu ma zai fuskanci kalubale mai tsanani a yankin.

Sai dai ya yi hasashen cewa Atiku Abubakar ba zai sha wahala sosai a Arewa ba, domin zai yi anfani da tasirin da yake da shi, da sarakunan gargajiya, da kasashen duniya, da kuma wasu tsoffin 'yan siyasa.

Ayodele ya kuma ce Atiku da Tinubu za su iya samun akalla kashi 25 cikin 100 na kuri'u a Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas.

A cewarsa, Tinubu zai kara yawan yakin neman zabe da farfaganda domin ya ci gaba da samun karbuwa da daidaito a yankin Arewa.

Kara karanta wannan

2027: Martanin Kwankwaso ga Ali Modu Sheriff bayan ya ce su Obi ba za su kai labari ba

Fasto ya yi hasashe kan zaben 2027
Babban malamin coci, Elijah Ayodele. Hoto: Elijah Babatunde Ayodele.
Source: Facebook

Tasirin Arewa a zaben 2027

Malamin ya ce Tinubu, Atiku da Obi duk suna bukatar goyon bayan jihohin Arewa domin samun nasara, yana mai cewa mutanen Arewa ne za su taka muhimmiyar rawa wajen tantance wanda zai lashe zaben.

Da yake magana kan Kano, Ayodele ya yi hasashen cewa babu wani dan takara da zai samu cikakkiyar nasara a jihar.

Ya ce duk wanda ya lashe Kano zai yi hakan ne da tazarar kuri'u kadan, yana kuma ikirarin cewa za a tauye wa Peter Obi wasu kuri'u a jihar, cewar Daily Post.

'Yadda za a kayar da Tinubu' - Ayodele

A baya, an ji cewa Fasto Elijah Ayodele ya bayyana dabarun da ya kamata ƴan adawa su yi idan suna son kayar da jam'iyya mai mulki a babban zaɓe na gaba.

Fitaccen limamin cocin ya faɗi dabarun ne a lokacin da ƴan siyasa suka fara shirye-shiryen zaɓen 2027 a Najeriya.

Ayodele ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai yi duk mai yiwuwa domin ya ci gaba da mulkin ƙasar nan har tsawon shekaru takwas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.