Matar Tinubu za Ta Tara Matan Kano Ta ba Su Tallafin Kayan Sana'a

Matar Tinubu za Ta Tara Matan Kano Ta ba Su Tallafin Kayan Sana'a

  • Gwamnatin Kano sanar da wani sabon tagomashi da uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu ta shirya raba wa wadansu daga cikin mata a jihar
  • Daraktar tattara bayanai ta Ofishin Gwamnan Kano, Gimbiya Nana Jibrin, ta sanar da shirin tallafa wa mata su fara sana'ar ƙosai bayan kalamanta a baya
  • Ta ce shirin ya samu kwarin gwiwa ne daga abin da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ke yi wajen ƙarfafa mata su rike sana'a hannu bibiyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Daraktar Tattara Bayanai ta Ofishin Gwamnan Kano, Gimbiya Nana Jibrin, ta sanar da wani sabon shiri na tallafa wa mata domin su fara sana'ar ƙosai a jihar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, 6 ga watan Yuli, 2026, Gimbiya Nana ta bayyana cewa shirin ya biyo bayan ƙoƙarin ƙarfafa mata da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ke yi a faɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Komai zai fito: APC na shirin fitar da bayanan mataimakin Tinubu a 2027

Oluremi Tinubu za ta tallafa wa mata a Kano
Sanata Oluremi Tinubu, matar shugaban kasa a Najeriya Hoto: Senator Oluremi Tinubu
Source: Twitter

Arewa Updates ta ruwaito cewa an zaɓi mata biyar da ke da sha'awar fara sana'ar ƙosai domin ba su cikakken horo a kan yadda za su kama sana'ar.

Kano: Remi Tinubu ta waiwayi masu kosai

Rahoton ya ce Gimbiya Nana Jibrin ta tabbatar da cewa za a horas da matan kan yadda ake haɗa garin ƙosai, yadda ake soya ƙosai mai inganci da ɗanɗano mai kyau, da kuma hanyoyin gudanar da kasuwanci yadda ya kamata.

A cewarta, shirin ba zai tsaya kan koyar da sana'a kaɗai ba, domin za a kuma taimaka wajen tallata kasuwancin waɗanda za su ci gajiyar shirin domin su samu kwastomomi cikin sauƙi.

Sanarwar ta bayyana cewa za a gudanar da tantance masu neman shiga shirin ne ta kafafen sada zumunta, inda masu sha'awa za su gabatar da buƙatunsu domin a zaɓi waɗanda suka cika ƙa'idojin da aka gindaya.

Gimbiya Nana ta kuma bayyana cewa Gwamnan Kano zai mara wa shirin baya domin tabbatar da nasararsa wanda ake sa ran zai taimaka wa matan su kama sana'a.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari: 'Manyan abubuwa 2 da tsohon shugaban ƙasa ya bari a Najeriya'

Za a karfafa wa masu sana'o'i a Kano

Ta ƙara da cewa bayan rukuni na farko ya fara gudanar da sana'arsu, gwamnati za ta ci gaba da zaɓen wasu mata domin su ma su amfana da irin wannan tallafi a matakai na gaba.

Za a zabi mata biyar a fara koya masu dabarun sayar da kosai a Kano
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

A cewarta, manufar shirin ita ce samar wa mata damar dogaro da kai ta hanyar sana'a, tare da ƙarfafa su wajen bunƙasa harkokinsu da ƙara samun hanyoyin shiga.

Shirin na daga cikin matakan da ake fatan za su taimaka wajen haɓaka ƙananan sana'o'i da bunƙasa tattalin arziƙin mata a jihar Kano, musamman masu sha'awar fara sana'a amma ba su da isasshen jari ko horo.

Remi Tinubu ta koma gona

A baya, kun samu labarin cewa rahotanni sun nuna uwargidan shugaban kasa Sanata Oluremi Tinubu ta sake girbe kayan lambu daga gonarta da ke Aso Rock Villa a babban birnin tarayya da ke Abuja.

Sanata Remi Tinubu ta buƙaci 'yan Najeriya su rungumi noma a cikin gida domin bunkasa samar da abinci da habaka tattalin arzikin al'umma wanda zairage kuɗin da maza ke kashewa tare da samar da lafiyayyen abinci ga iyalansu.

Kara karanta wannan

Dan a mutun Tinubu ya kare Oluremi, ya ba da labarin attajira mai sayar da ƙosai a Abuja

Sanata Oluremi Tinubu ta kuma nuna amfanin gonar da ta girba, ciki har da alayyahu, rama da ugu, tana mai cewa noman gida hanya ce mai sauƙi kuma mai araha ta samun lafiyayyen abinci da zai gina jiki a cikin sauki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng