‘Abin da Tinubu Ya Kamata Ya Yi wa Gbajabiamila kafin Binciken ICPC’: Atiku
- Hadimin Atiku Abubakar shawara kan yada labarai ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Femi Gbajabiamila
- Paul Ibe ya ce barin wadanda ake zargi su ci gaba da zama a mukamansu yayin bincike na iya ba su damar yin katsalandan
- Fadar Shugaban Kasa ta ce PFIPC ba hukuma ce ta halal ba, duk da tambayoyi kan kasafin kudinta da asusun da aka bude a CBN
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Paul Ibe, mai ba tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar shawara kan yada labarai ya yi magana kan ma'aikatar bogi a Najeriya.
Ibe ya soki umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bai wa Hukumar ICPC na binciken Hukumar PFIPC ba tare da dakatar da jami'an da ake alakanta da lamarin ba.

Source: UGC
Hakan na cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata 7 ga watan Yulin shekarar 2026 da muke ciki.
Ma'aikatar bogi: Shawarar hadimin Atiku ga Tinubu
Ibe ya bayyana cewa bai dace ba shugaban kasa ya ba da umarnin bincike ba tare da dakatar da manyan wadanda ake zargi ba, ciki har da Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila.
Ya ce rashin dakatar da duk wadanda ake dangantawa da abin da ake kira badakalar #GbajaGate yana nufin kamar su ne za su zama alkalai a kan shari'arsu.
A cewarsa, ci gaba da zamansu a ofis yayin gudanar da binciken na iya ba su damar yin katsalandan ko tasiri kan yadda binciken zai gudana.

Source: Facebook
Atiku ya bukaci binciken ma'aikatar bogi
Tun da farko, Shugaba Tinubu ya umurci Hukumar ICPC da ta gudanar da cikakken bincike kan PFIPC, wadda Fadar Shugaban Kasa ta bayyana a matsayin hukuma ta bogi da ba ta da wata kafa ta doka ko amincewar shugaban kasa.
Shugaban kasar ya kuma bai wa hukumar kwanaki 30 domin kammala binciken tare da mika rahotonta ga gwamnati.
PFIPC ta jawo cece-kuce ne bayan Prince Adeniyi Adeyemi Matthew, wanda ke ikirarin shi ne Darakta Janar na hukumar, ya ce ya biya naira miliyan 600, ciki har da naira miliyan 400 ta hannun wasu mutane, domin samun mukamin.
Har ila yau, Adeyemi ya zargi Gbajabiamila da neman kashi 48 cikin 100 na kudin da aka ware domin fara ayyukan hukumar.
Sai dai Fadar Shugaban Kasa ta yi watsi da ikirarin Adeyemi, tana mai cewa shi dan damfara ne, tare da jaddada cewa PFIPC ba ta wanzu a hukumance.
Kiran da Ibe ya yi ya kara matsin lamba kan Fadar Shugaban Kasa, yayin da jam'iyyar NDC da tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, su ma suka bukaci a dakatar da Gbajabiamila har sai an kammala binciken.
Ma'aikatar bogi: Ana kiran Tinubu ya kori wasu
An ji cewa kungiyar CNPP ta bukaci a kori manyan jami'an gwamnatin tarayya bayan abin kunya na ma'aikatar bogi da aka ce an samu a Najeriya.
Hukuma mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council ta samu kudi har N1.3bn a kasafin kudin 2026 duk da cewa ta bogi ce.
CNPP ta yi gargadi cewa gwamnati ba ta da ikon soke dokar da ta gabatar da ita da kanta ta hanyar sanarwa ga 'yan jarida kawai.
Asali: Legit.ng

