"Ba Gaskiya ba ne": APC Ta Karyata cewa 'Ya'yanta Sun Koma wajen Kwankwaso

"Ba Gaskiya ba ne": APC Ta Karyata cewa 'Ya'yanta Sun Koma wajen Kwankwaso

  • Jam'iyya mai mulki ta APC a jihar Kano ta musanta rahotannin cewa 'ya'yanta sun tururwan rabuwa da ita zuwa NDC da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ke ciki
  • Jam'iyyar ta bakin mai magana da yawunta Auwalu Soja ta ce babu wata hujja da ke tabbatar da zargin, tare da cewa waɗanda aka nuna ba a san su a cikinta ba
  • APC ta bayyana cewa har yanzu tana da ƙarfinta, tana mai cewa masu kaɗa ƙuri'a ba za su ruɗu da siyasar 2027 ba saboda sun san wa za su zaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta yi fatali da rahotannin da ke cewa 'ya'yanta a ƙaramar hukumar Kumbotso sun fice zuwa NDC.

Kara karanta wannan

Abin da gwamnatin Tinubu ta ce kan ba hukumar bogi kudi, bude asusu a CBN

Sakataren yaɗa labarai na APC a jihar Kano, Auwalu Soja, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba 8 ga watan Yuli, inda ya ce suna da karfi a Kumbotso.

APC ta karyata cewa yayanta sun koma NDC
Shugaban APC Yilwatda Nentawe, dandazon taron yan APC, Shugaban Kwankwasiyya Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda/Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Daily Trust ta kawo labarin cewa Auwalu Soja ya ce rahotannin da ke yawo ba su da tushe balle makama, yana kuma zargin tafiyar Kwankwasiyya da yaɗa farfaganda.

Zargin da APC ta yi wa NDC

Jaridar Punch ta kawo labarin cewa APC a Kano ta zargi NDC da yada labarin karya domin karkatar da hankalin jama'a daga matsalolin cikin gida da take fuskanta.

A cewarsa, APC na ci gaba da samun goyon bayan 'ya'yanta a karamar hukumar Kumbotso, yana mai cewa jam'iyyar ba ta da wani bayani kan mutanen da ake ikirarin sun sauya sheƙa.

Auwalu Soja ya ce APC ta Kumbotso tana tsintsiya madaurinki daya kuma tana biyayya ga shugabancin jam'iyyar, tare da bayyana cewa babu wata sahihiyar hujja da ke nuna an samu ficewar 'ya'yanta da yawa a lokaci gudaa yankin.

An yaba aikin gwamntin APC a Kano

Haka kuma, Awalu Soja ya ce 'yan APC sun yaba wa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, kan jawo zuba hannun jari zuwa Kumbotso domin bunƙasa tattalin arziki da samar wa matasa guraben aikin yi.

Kara karanta wannan

Komai zai fito: APC na shirin fitar da bayanan mataimakin Tinubu a 2027

APC ta yabi ayyukan gwamna Abba Kabir Yusuf
Aikin titi a jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

APC ta buƙaci tafiyar Kwankwasiyya ta mayar da hankali wajen warware matsalolin shugabanci da take fuskanta maimakon abin da ta kira yaɗa farfaganda marar tushe.

Jam'iyyar ta kuma bayyana cewa al'ummar Kano ba za su bari a ruɗe su da dabarun siyasa ba yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.

APC ta roƙi mazauna Kumbotso da su yi watsi da rahotannin da ke ikirarin an samu ficewar 'ya'yanta da yawa daga jam'iyyar, tana mai jaddada cewa har yanzu tana da ƙarfi kuma tsarinta yana nan daram a ƙaramar hukumar.

APC: Shugaban karamar hukuma ya yi murabus

A baya, kun ji cewa shugaban ƙaramar hukuma a jihar Sakkwato ya sanar da cewa ya hakura da ci gaba da rike kujerar da ya ke kai, tare da mika takardar ajiye aiki ga jam'iyyarsa da gwamantin Ahmed Aliyu.

Isa Kalanjeni da kansa ne ya yi murabus daga kujerar, sannan ya bayyana cewa ya fice daga APC ne saboda dalilin kashin kai yayin da ya bar shugabancin karamar hukumar Tangaza saboda matsalolin gudanarwa.

Kara karanta wannan

"Ni ba ungulu ba ne:" Ganduje ya yi martani ga zargin zai hade da Kwankwaso

Duk da ya sanar da dalilinsa na hakura da jam'iyya mai mulki ta APC da kujerarsa, gwamnatin jihar Sakkwato karkashin Ahmed Aliyu ba ta fitar da sanarwa game da wannan gagarumin sauyi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng