APC Ta Karbe Mutumiyar Atiku Abubakar da Ta Sauya Sheka daga Jam’iyyar ADC
- Gimbiya Aslam Aliyu ta hakura da tafiyar Atiku Abubakar jim kadan bayan ya samu takara a jam’iyyar ADC
- Tsohon mataimakin shugaban kasar kuma jagoran adawa ya rasa daya daga cikin mata da ake ji da su a siyasa
- Dr. Aslam ta ce ‘yan adawa ba su da wani manufa ta a zo – a gani, saboda haka sai ta bi Bola Ahmed Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Zamfara - Aslam Aliyu wanda mutumiyar Atiku Abubakar ce a jihar Zamfara, ta sauya sheka daga jam’iyyar hamayya ta ADC zuwa APC.
Aslam Aliyu ta kawo karshen rade-radin da aka rika ji kwanaki cewa ta canza gida, a karshe aka gano cewa labarin sam ba gaskiya ba ne.

Source: Facebook
Aslam Aliyu ta raba gari da Atiku Abubakar
Rahoton The Cable ya tabbatar da ficewar Aslam Aliyu daga jam’iyyar ADC mai adawa a Najerya.
A wani jawabi da ta fitar ranar Lahadi, 5 ga watan Yuli 2026, ‘yar siyasar ta ce ta dauki matakin ne bayan nazarin tafiyar siyasar kasar.
Jawabin da ta fitar ya bayyana cewa tun da ta ke da Alhaji Atiku Abubakar na kusan shekaru 20, imaninta a gare shi bai taba yin rawa ba.
“Na tsawon kusan shekaru 20, na yi aiki babu kakkautawa a bangaren Mai girma Atiku Abubakar, ‘dan takarar shugaban kasa na ADC a 2027.
A duk tsawon wannan lokaci, ba a taba samu imanina ya yi rawa ba,”
Meyasa Aslam ta rabu da gidan Atiku?
Ba komai ya sa Gimbiya Aslam Aliyu barin gidanta a wannan lokaci ba, illa abin da ta kira rashin manufa, tana ganin ba a san inda aka dosa ba.
“Sai dai, bayan kusan shekaru 20 na aiki tukuru, ya tabata karara cewa ‘yan adawa ba su da wata manufar kwarai ko kuma dabarar ceto kasa mai bullewa.”
Da alama dai wannan labari ya yi wa ‘ya ‘yan APC dadi saboda tasirin Aslam a gidan Atiku kuma ganin cewa mace ce da ta yi suna a siyasa.
Wani shafi na masoyan Bola Tinubu mai suna Jagaban Army a dandalin Facebook ya sanar da labarin.
‘Yar siyasar da aka haifa a Zamfara ta ce ADC ba ta san komai ba ban da sukar gwamnati ba tare da sun kawo wata mafita da za ta ceci Najeriya ba.
Jam'iyyar APC ta dauke Aslam daga ADC
A ganinta, lokaci ya yi da za a daina suka mara amfani don haka sai ta shiga jam’iyyar APC shekaru uku bayan an dakatar da su daga jam'iyyar PDP.
Daga yanzu tana goyon bayan Bola Ahmed Tinubu gadan-gadan kuma ta bukaci matasa, mata da sauran ‘yan Najeriya masu kishin kasa su biyo ta.
A matsayinta na uwa, ta na so a mara wa Tinubu baya wanda ta ce babu mai iya doke shi a 2027, ta ce da yardar Allah shi ne dai zai koma fada Aso Rock.
Shugaban APC a nasa bangaren, ya ji dadin wannan labari, yana mai maraba Gimbiya Dr. Aslam Aliyu, ya kuma ce zuwanta zai taimaki jam'iyya mai mulki.
Nentawe Yilwatda ya yi magana ne a shafinsa na Facebook, ya ce APC tana alfahari da shigowar Aslam.
ADC na neman shiga rudani a jihar Kaduna
Matar El-Rufai ta yi magana bayan bullar ‘sautin’ Isa Ashiru yana sukar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai kamar yadda aka samu labari.
Wasu ‘yan ADC da kuma Hajiya Aisha El-Rufai sun ce babu gudu babu ja da baya a goyon bayan Isa Ashiru Kudan duk da bayyanar wani sauti kwanan nan.
Ganin an shigo wani zamani na cigaban fasaha a duniya, mutanen Isa Ashiru Kudan sun ce kirkirar sautin aka yi saboda a bata masa suna a jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng


