‘Dan Takarar Gwamna a PDP bai Son Tazarce Ya Ce Wa’adi 1 Rak Ya Ishe Shi
- Ifeanyi Odili ya tsaya takarar neman gwamna a Ebonyi a zabe mai zuwa, yana sa ran kawo karshen mulkin APC a jihar
- ‘Dan takarar jam’iyyar hamayyar ya jero ayyukan da zai yi wa jiharsa muddin al’umma suka ba shi amanar kuri’unsu
- Odili ya duaki alkawarin gyara bangaren kiwon lafiya, samar da wutar lantarki kuma ya rage adadin matasa marasa aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Ebonyi - Ifeanyi Odili mai neman takarar gwamnan jihar Ebonyi a karkashin jam’iyyar PDP a 2027 ya ce wa’adi guda kurum zai yi a ofis.
Idan da za a zabe shi a shekara mai zuwa, Ifeanyi Odili ya yi alkawarin zai yi wa’adi guda ne a matsayin gwamna, ba tare da ya zarce a mulki ba.

Source: Getty Images
Mai neman takara a PDP bai son tazarce
Da yake magana da ‘yan jarida a Legas a ranar Asabar, The Cable ta ce ‘dan takarar ya zayyano abubuwan da za iyi idan har ya zama gwamna.
"Na fada wa Ubangiji da ni karon kai na cewa ina son in zama gwamnan farko da ba zai nemi tazace bayan shekaru hudu ba.
Abin da hakan yake nufi shi ne na tattaro abubuwan da na ke so in yi wa Ebonyi cikin shekaru hudu.
- Ifeanyi Odili
An fara rabu wa da siyasar jam'iyya
‘Dan takarar gwamnan na PDP ya ce siyasar Najeriya ta fara sauyawa daga biyayya ga jam’iyya zuwa la’akari da ‘dan takara da irin cancantarsa.
Saboda haka ne Mista Ifeanyi Odili ya ce yake samun mabiya daga bangaren kowace jam’iyya.
‘Dan siyasar ya ce farin jinin da yake samu a halin yanzu, ya razana jam’iyyar APC mai mulkin Ebonyi, hakan ya sa yake hango nasara a 2027.
Mista Ifeanyi Odili yake cewa:
"Muna da ‘yan adawa rututu da suke yin murabus suna shigowa cikinmu. Yanzu haka da na ke magana, ana rusa wasu tsarin, har da wasu jam’iyyu.
"Ba zancen siyasar jam’iyya ake yi ba a yanzu kuma. Najeriya za ta cigaba tare da la’akari da wane ne ‘dan takara, me ka yi a baya kuma me ka zo da shi."

Source: Getty Images
Abubuwan da 'dan takaran ya yi alkawarin yi
A shafin gidan rediyo Najeriya, an ruwaito Odili yana jero irin abubuwan da zai shimfida wa mutanen Ebonyi a bangarorin rayuwa dabam-dabam.
Odili ya sha alwashin gyara bangaren kiwon lafiya ta hanyar daukar ma’aikata, kara darajar manyan asibitoci da inganta kwarewar malaman lafiya.
Idan ya ci zabe, zai bada fifiko a bangaren noma, samar da ayyukan yi ga matasa, harkokin yawon bude ido tare da ganin an samar da wuta da ba a daukewa.
Ban da watsi da tsarin siyasar jam’iyya, Odili bai goyon bayan karba-karba da ake yi a mulki, yana tunanin cewa hakan ne ya hana Ebonyi cigaba.
A cewarsa ba a taba yin wani tsari da ya ce za a rika zagaya wa da mulki tsakanin yankunan da ake da su a jihar ba, ya ce an daina irin wannan tunani.
An kama 'dan takarar gwamna a PDP
Tsohon ministan Bola Tinubu mai neman takarar gwamna a 2027 zai yi kwana akalla 14 a ragar ICPC kamar yadda labari ya gabata tun a kwanaki.
Uche Nnaji ya shiga hannu a dalilin binciken shi da ake yi amfani da takardun karatu da bogi da kuma na kammala yi wa kasa hidima wato NYSC.
Matsalolin tsohon ministan kimiyya sun karu da kotu ta ba ICPC damar rike shi na kwana 14. Hakan zai ba hukumar damar yi masa tambayoyi.
Asali: Legit.ng


