Yadda Hadu wa da Peter Obi zai Jawo wa Kwankwaso Asarar Kuri'a a 2027

Yadda Hadu wa da Peter Obi zai Jawo wa Kwankwaso Asarar Kuri'a a 2027

  • Tsohon gwamnan Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ce Peter Obi ba zai samu goyon bayan mafi yawan masu kada kuri'a daga Arewa ba a zaben 2027
  • Ya bayyana cewa duk da an samu hadin kai a tsakanin Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wannan ba zai jawo hankalin Kanawa wajen zaben yan takarar ba
  • Ali Modu Sheriff ya kuma bayyana cewa a yanzu haka, mutanen Kano za su juya wa zaben Kwankwaso bayya matukar yana a matsayin mataimakin shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos – Jigo jam'iyyar APC ya kare salon tafiyar gwamnatin Bola Tinubu kan matsalar tsaro, yana mai cewa kalubalen da ake fuskanta matsala da aka gada daga gwamantin baya.

Sanata Ali Modu Sheriff, wanda tsohon gwamnan jihar Borno ne ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ba zai samu goyon bayan masu kada kuri'a daga Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

"Yana son raba Najeriya"; Sheriff ya soki Peter Obi kan neman Tinubu ya yi murabus

Ali Modu Sheriff ya ce haduwa da Obi ya zama matsala ga Kwankwaso
Yan takarar shugaban kasa da mataimaki a NDC Peter Obi da Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Ali Modi Sheriff ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television ranar Litinin, 6 ga watan Yuli, 2026.

Ali Modu Sheriff ya magantu kan Obi

Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa Ali Modu Sheriff ya kuma kare matakan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke ɗauka wajen magance matsalar tsaro a ƙasar nan.

Da yake magana kan damar Obi, tsohon gwamnan ya ce bai damu da takararsa ba domin yana da yakinin cewa mafi yawan masu kada kuri'a daga Arewa ba za su mara masa baya ba.

Lokacin da aka tuna masa cewa Obi ya samu kuri'u masu yawa a jihohin Filato da Nasarawa a zaben 2023, Ali Modu Sheriff ya ce halin da ake ciki yanzu ya bambanta da na wancan lokaci.

Kwankwaso ya rasa goyon baya - Ali Modu Sheriff

Sanata Ali Modu Sheriff ya kuma yi ikirarin cewa magoya bayan tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba sa son a yi wata kawance ta siyasa da Peter Obi.

Kara karanta wannan

Hadimin mataimakin shugaban majalisa ya yi murabus, ya koma bayan abokin hamayyarsa

A cewarsa, wasu daga cikin magoya bayan Kwankwaso a Kano sun bayyana cewa za su ci gaba da goyon bayansa idan ya tsaya takarar shugaban kasa, amma ba za su mara masa baya ba idan ya hada kai da Obi.

Ali Modu Sheriff ya zargi Peter Obi da korar yan Arewa daga Anambra
Tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff Hoto: Ajid Saleh Ajid
Source: Facebook

A kalamansa:

"Yanzu lamarin ya sauya. Lokacin da Peter Obi yake gwamnan jihar Anambra, ya kori 'yan Arewa daga jihar Anambra."
"Abin da mutanen Kano ke gaya wa Kwankwaso ke nan a yanzu. Suna cewa sun dade suna mara masa baya, kuma za su ci gaba da yin hakan idan ya tsaya takarar shugaban ƙasa, amma ba za su goyi bayansa ba idan ya haɗa kai da Peter Obi."

Zargin Ali Modu Sheriff kan Obi

A baya, mun kawo labarin cewa a cikin 'yan kwanakin nan, Peter Obi, ya rika fitowa yana neman shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus daga mukaminsa saboda matsaloli a Najeriya.

Amma tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, wanda jigo ne a APC ya fito ya yi martani ga dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar NDC a zaben 2027, inda ya ce ba shi da bakin magana.

Ali Modu Sheriff ya bayyana cewa Peter Obi shi ne mutum mafi rashin cancanta da zai fito ya nemi Shugaba Tinubu ya yi murabus ganin yadda ya ke da akidar neman a raba Najeriya ta 'Biafra'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng