ICPC: Jam'iyyar ADC Ta Jero Bukata 6 da Ta Yi Maganar Mugun Halin da El Rufai ke ciki
- Kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya fitar da jawabi game da rikon da hukumar ICPC ta ke yi wa Nasir El-Rufai
- Jam’iyyar hamayya ta ADC ta yi zargin cewa an hana tsohon gwamnan Kaduna haduwa da lauyoyi har da iyalinsa
- A kokarin hana shi zuwa asibiti, Bolaji ya ce jami’an ICPC sun kama likitan El-Rufai sannan aka gwabje matarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Jam’iyyar hamayya ta ADC ta fito ta nuna fargabar ta a game da halin da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya shiga.
ADC ta zargi hukumar ICPC da karya dokoki yayin da ta ke cigaba da tsare Malam Nasir El-Rufai na tsawon wata da watanni a Najeriya.

Source: UGC
A wani jawabi na musamman da aka fitar a shafin X ta hannun Bolaji Abdullahi, ana zargin ICPC ta hana Nasir El-Rufai ganin likitansa.
Baya ga matsalar lafiya, jam’iyyar ta ce hukumar da ta ke yaki da rashin gaskiya ta cafke likitan da yake duba tsohon gwamnan Kaduna.
Abin bai tsaya a nan ba, sanarwar ta yi bayanin cewa an ci zarafin wata daga cikin matan El-Rufai a babban birnin tarayya wato Abuja a jiya.
Bola Abdullahi ya ce:
"An shirya cewa El-Rufai zai je a duba shi a babban asibitin kasa na Abuja a yau (Talata). Amma sai aka saba maganar asibiti duk da tabarbarewar lafiyar shi,
"Jami’an ICPC suka dage sai sun maida shi inda ake tsare shi. Da likitansa da matarsa suka nuna adawa da hakan, wannan ya jawo sa-in-sa har aka doke matar sa"
ADC ta jefi Gwamnatin Bola Tinubu da zargi
A kafar X, Bello El-Rufai ya fitar da jawabin da Kakakin ADC na kasa ya yi, yake cewa wannan danyen aiki na ICPC da gwamnati ya wuce gona da iri.
Sanarwar ta zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da yi wa dokar kasar mutane miliyan 200 hawan kawara saboda zargin keta hakkin Bil Adama.
Jam’iyyar adawar ta ce ya kamata a san shugaba Bola Tinubu yana rike Nasir El-Rufai ne saboda sabanin siyasa duk da ana karkashin farar hula.
"Babu gwamnatin damukaradiyya da ta ke ikirarin bin doka da za ta hana wanda aka tsare zuwa asibiti ko a hana shi ganin iyalin shi na kusa.
"Wannan yanayi saba wa kotu ne karara domin sun ba shi damar ganin lauyoyi, likitoci da iyalinsa ba tare da wani kaidi ba."
- Kakakin ADC
Bukatu 6 da jam'iyyar ADC ta gabatar
Mai magana da yawun ADC ya kara da cewa a gwamnatin kama-karya ne ake yin irin wannan abin, kuma ba zancen El-Rufai kawai ake yi ba.
"Yau El-Rufai ne. gobe zai iya zama kowane ‘dan Najeriya wanda laifinsa shi ne saba wa masu mulki."
ADC ta nemi jin da umarnin wa aka hana El-Rufai ganin likita ta kuma nemi a kyale shi ya rika ganin iyalinsa kuma a binciki sharudan belinsa.
Sai ta bukaci a janye takunkumin da aka kakaba, sannan a bi ka’idoji, ICPC ta yi aiki da gaskiya kuma a daina yakarsa da hukumomin gwamnati.
ICPC ta kama likitan Malam Nasir El-Rufai
Ana da labari Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa ta zargi tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da saba sharuddan ziyarar asibiti,
Hukumar ta kama likitansa, Farfesa Bello Abubakar, bisa zargin bayar da bayanan karya lokacin da ake binciken tsohon gwamnan na jihar Kaduna a kotu.
Ko da yake ICPC ta amince da ziyartar asibitin, daga baya ta gano wasu hotuna a Facebook da wani makusancinsa, Isa Ashiru Kudan a zaman siyasa.
Asali: Legit.ng


