Rahoton WFP: ADC Ta Zargi Tinubu da Jefa Miliyoyin Mutane cikin Yunwa a Jihohin Arewa 9
- Jam'iyyar adawa ta ADC ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kara jefa mutane cikin yunwa a Najeriya
- Jam’iyyar ta ce rahoton Majalisar dinkin duniya ya nuna fiye da mutum miliyan 17 na fama da matsananciyar yunwa a wasu jihohin Arewa
- Ta danganta matsalar da rashin tsaro, hare-haren 'yan ta'adda kan manoma da hauhawar farashin abinci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam’iyyar ADC ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da haddasa karuwar matsananciyar yunwa, wacce ta bayyana da 'bala'in jin kai".
ADC ta kafa hujja da rahoton hukumar abinci ta Majalisar dinkin duniya (WFP) da ya nuna cewa fiye da mutum miliyan 17 na fama da matsananciyar yunwa a jihohin da rikici ya shafa a Najeriya.

Kara karanta wannan
Tinubu ya waiwayi manyan kamfanonin kafafen sadarwa, za a binciki Meta, X da sauransu

Source: Facebook
A rahoton Leadership, ADC ta ce matsalar ƙarancin abinci ta samo asali ne daga gazawar gwamnatin tarayya wajen magance rashin tsaro, kare manoma da kuma aiwatar da manufofin da za su rage tsadar kayan abinci.
ADC ta ce rahoton WFP ya tona asiri
Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da sakataren yaɗa labarai na ADC ta ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar a jiya Litinin domin mayar da martani kan sabon rahoton WFP.
Rahoton ya nuna cewa sama da mutum miliyan 17 a jihohi tara na Arewa da rikici ya shafa na cikin mawuyacin hali na rashin abinci, lamarin da ya karu da kusan mutum miliyan biyu idan aka kwatanta da hasashen da aka yi a baya.
Da take martani, ADC ta ce:
"Waɗannan ba alkaluman jam’iyyar adawa ba ne, kuma ba taken yaƙin neman zaɓe ba ne. Wannan rahoto ne daga babbar hukumar jin kai ta duniya mai kula da batun yunwa."
ADC ta ɗora laifi kan gwamnatin APC
ADC ta ce rahoton ya nuna ƙarara cewa rashin tsaro, hare-hare kan manoma, raba jama'a da muhallansu, ƙarancin damar kai agajin jin kai da kuma raguwar tallafi ga masu buƙata ne suka haddasa matsalar.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa:
"Yunwar da miliyoyin ‘yan Najeriya ke fama da ita ba bala’in dabi’a ba ne. Bala’in jin kai ne da gwamnatin APC ta haddasa."
Ta kuma ce gwamnatin Tinubu ta gaza kare rayuka da gonaki, lamarin da ya jawo ƙarancin noma da tsadar rayuwa, cewar rahoton tashar This Day.

Source: Twitter
ADC ta yi alƙawarin magance matsalar
Jam’iyyar ADC ta ce idan ta samu mulki, za ta ɗauki batun tsaron abinci a matsayin wani muhimmin ɓangare na tsaron ƙasa.
Ta ce za ta ba ƙananan manoma fifiko ta hanyar samar musu da ingantattun iri, taki, injinan noma, horo da kuma hanyoyin kasuwanci domin ƙara yawan amfanin gona da rage tsadar abinci.
Haka kuma, ADC ta yi alƙawarin farfaɗo da madatsun ruwa 264 da aka yi watsi da su domin bunƙasa ban ruwa a duk shekara da ƙara yawan amfanin gona.
Atiku ya yi zargin kullawa ADC tuggu
A wani rahoton, kun ji cewa 'dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya yi zargin cewa ana ana kulla wani shiri da zai hana jam'iyyarsa shiga zaben 2027.
Atiku ya bayyana cewa sun gano akwai wani yunkurin amfani da bangaren shari'a da hukumomi wajen raunana jam'iyyar adawa ta ADC.
Ya ce duk da yana fatan wannan zargi ba zai zama gaskiya ba, abubuwan da suka faru a siyasar Najeriya a baya sun sa ba za a iya yin watsi da irin wannan lamari ba.
Asali: Legit.ng

