Atiku Ya Yi Zargin ana Shirya Masu Gadar Zare, Za a Hana ADC Shiga Zaben 2027

Atiku Ya Yi Zargin ana Shirya Masu Gadar Zare, Za a Hana ADC Shiga Zaben 2027

  • 'Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC Alhaji Atiku Abubakar ya yi zargin cewa ana ana kulla wani shiri da zai hana jam'iyyarsa shiga zaben 2027
  • Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa sun bankado akwai yunkurin amfani da shari'a da hukumomi wajen raunana jam'iyyar adawa
  • Ya bayar da shawara ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da bangaren shari'a a kan yadda za su kauce wa zama 'yan abi yarima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa akwai wasu mutane a cikin masu mulki da ke ƙoƙarin hana jam'iyyar ADC shiga babban zaɓen 2027.

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban mai taimaka masa kan hulɗa da jama'a, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Litinin 29 ga watan Yuni, 2026.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan shari'ar NDC, ya aika sako ga magoya baya

Atiku ya ce an bankado shirin gwamnati a kan ADC
Shugaban kasa Bola Tinubu, Alhaji Atiku Abubakar Hoto: Bayo Onanuga/Atiku Abubakar
Source: Twitter

Jaridar Punch ta kawo labarin cewa Atiku ya ce ya samu sahihan bayanai da ke nuna cewa ana haɗa kai ta fannin siyasa da shari'a domin hana ADC bayyana a takardar kaɗa ƙuri'a a zaɓen 2027.

Ana shirin hana ADC takara - Atiku

A ruwayar The Cable, Alhaji Atiku Abubakar ya ce tuggun da ake hada wa na daga cikin wani shiri na raunana jam'iyyun adawa tare da hana 'yan Najeriya damar zaɓar shugaban ƙasar da suke so cikin 'yanci.

Ya bayyana cewa:

"Mun san dukkannin shirye-shiryensu. Yayin da suke ƙoƙarin haddasa rikici a cikin jam'iyyun adawa, mun san ainihin abin da suke son kai wa hari shi ne ADC, domin ita ce mafi sahihancin madadin da ake da ita."

Atiku ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya, ba tare da la'akari da jam'iyyarsu ba, da su yi tir da duk wani yunƙuri na bai wa jam'iyya mai mulki damar zaɓar waɗanne jam'iyyun adawa za su shiga takara.

Kara karanta wannan

'Za a kayar da Tinubu warwas a zaben 2027,' Sanata Dickson na NDC

Kiran Atiku ga hukumar INEC

Atiku ya ce duk da yana fatan wannan zargi ba zai zama gaskiya ba, abubuwan da suka faru a siyasar Najeriya a baya sun sa ba za a iya yin watsi da irin wannan gargaɗi ba.

Ya yi zargin cewa ana yawan jawo hukumomin da ya kamata su kasance masu zaman kansu cikin rikicin siyasa, tare da amfani da ƙararrakin da ba su da tushe, matakan gwamnati da matsin lamba wajen takura wa 'yan adawa.

Atiku ya kuma zargi gwamnatin APC da mayar da hankali kan siyasa maimakon magance matsalolin tattalin arziki da tsaro da ke addabar ƙasar.

Atiku ya ba INEC da bangaren shari'a shawara a kan ADC
Alamar jam'iyyar ADC da 'dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Ya ce:

"A lokacin da 'yan Najeriya ke fama da yunwa, hauhawar farashi, rashin aikin yi, matsalar tsaro da raguwar ƙarfin saye, masu riƙe da madafun iko sun fi mayar da hankali kan kare makomarsu ta siyasa maimakon ceton ƙasa."

Sakon Atiku ga Tinubu

A baya, mun ruwaito cewa 'dan takarar shugaban kasa a babban zaben 2027, Alhaji Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da yunkurin maida Najeriya tsarin jam'iyya daya.

Kara karanta wannan

2027: 'Yan takarar NDC sun gamu da matsala bayan INEC 'ta hana' a shigar da sunayensu

Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne a Najeriya ya nuna damuwa kan yunkurin soke rijistar jam'iyyar hamayyya ta NDC ta hanyar amfani da kotu ana dab da hura kogen zaben 2027 mai zuwa.

Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci Shugaba Tinubu ya yi koyi da tsofaffin shugabannin Najeriya, kamar su marigayi Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan, wadanda suka ba wa 'yan adawa 'yancin siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng